Omoyele Sowore ya bayyana cewa zai daina cin abinci har sai DSS ta sake shi

Omoyele Sowore ya bayyana cewa zai daina cin abinci har sai DSS ta sake shi

Shugaban jam'iyyar African Action Congress AAC kuma jagoran kungiyar juyin juya hakin #RevolutionNow, Omoyele Sowore, ya kaddamar da yajin cin abinci a ofishin hukumar DSS da ta tsareshi kimanin kwanaki 100 yanzu.

Sowore ya kaddamar da yajin ne domin nuna bacin ransa kan abinda ya siffanta a matsayin take masa hakkinsa na dan Adam.

A ranar Laraba, Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umurnin sakin, Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar ADC a zaben Fabrairun 2019 kuma jagoran 'yan neman juyin juya hali wato #RevolutionNow.

A baya, lauyansa, Femi Falana (SAN) ya ce an cika dukkan ka'idojin bayar da belinsa da kotu ta gindaya.

Femi Falana ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba, inda yace Omoyele Sowore tare da abokina Olawale Bakare sun cika sharuddan beli a kan tuhume tuhumen cin amanar kasa da gwamnatin Najeriya ke musu.

Hukumar tsaro na DSS a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba ta karyata rahotannin cewa ta ki ba umurnin kotu hadin kai wacce ta bukaci a bayar da belin jagoran zanga-zangar juyin-juya hali, Omoyele Sowore.

Amma har yanzu yana tsare a ofishin hukumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel