Dalilin da yasa na sha kaye a kotun daukaka kara - Tsohon gwamnan APC

Dalilin da yasa na sha kaye a kotun daukaka kara - Tsohon gwamnan APC

Dan takarar kujerar sanata a karkashin jam'iyyar APC a zaben 23 ga watan Fabrairu a jihar Delta, Dr. Emmanuel Uduaghan, yace, ya fadi akotun daukaka kara ne sakamakon matsalolin da ya samu tun kafin zabe.

A takardar da yasa hannu da kanshi, Uduaghan yace, ya karbi hukuncin kotun daukaka karar da hannu bibbiyu kuma ya taya sanata James Manager murnar nasararsa.

Yayi bayanin cewa, alkalan kotun daukaka karar sun yi hukuncinsu ne akan abinda ya faru kafin zabe wanda aka kawo shi kotun daukaka kara ba tsare da an dubashi a kotun sauraron kararrakin zabe ba.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa hukumar kwastam ta hana kai man fetur garuruwa kusa da iyako

Uduaghan yace: "Na fadi a kotun daukaka kara ne saboda abubuwan da suka faru kafin zabe wanda kotun tayi hukunci akansu. Ba a dubesu ba a kotun sauraron kararrakin zabe ba inda a can ne yakamata duk kararrakin aji su. Kotun ta yanke hukunci kuma na karba da hannu bibbiyu."

A maida martanin gaggawa da tsohon gwamnan yayi bayan hukuncin, ya yi kira ga magoya bayansa da ke mazabar da kada jikinsu yayi sanyi sai kwarin guiwa da yake bukatar su samu. An samu gogewa a faruwar lamarin.

A ranar Litinin ne kotun daukaka kara ta yi watsi da karar tsohon gwamnan da ke kalubalantar nasarar Sanata Manager tare da soke hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Delta wacce ta soke zaben yankin kuma ta bada umarnin yin sabon zabe.

Tsohon gwamnan yayin da yake tuna yakin neman zabensa na 2014, yace nasararsa ta samo asali ne daga zaman lafiyan da ke wanzuwa tsakanin kabilu daban-daban na kasar nan dake yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel