FG tace babu amincewarta wani tsohon gwamna kuma sanata a yanzu ya shigo da makamai

FG tace babu amincewarta wani tsohon gwamna kuma sanata a yanzu ya shigo da makamai

Gwamnatin Najeriya ta tabbatarwa da jaridar premium Times cewa, tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya shigo da makamai Najeriya ne ba tare da izinin gwamnati ba.

Amosun, wanda a halin yanzu sanata ne, ya bukata kuma ya samu izinin shigo da motocin yaki 13 ne kacal don amfanin 'yan sandar jihar Ogun a 2012. Ben Akabueze, darakta janar na ofishin kasafin kudi na tarayya, ya sanar da jaridar Premium Times a wata wasika da ya aiko mata a cikin kwanakin nan.

A watan Yuni ne jaridar Premium Times ta fara fallasa yadda asirin Amosun ya tonu bayan da ya shigo da motocin yaki, bindigogi kirar AK47 1,000, miliyoyin alburusai, rigunan da alburushi baya fasawa da hular kwanon 'yan sanda ba tare da yardar gwamnati ba.

Majiyar tsaro da tayi magana da Premium Times tace akwai lauje cikin nadi a lamarin.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa na sha kaye a kotun daukaka kara - Tsohon gwamnan APC

Majiyar tace an sa ma Amosun din ido don tsoron kada ya ba 'yan bangar siyasa makaman tare da sauran 'yan ta'adda a zaben 2019 da ya gabata.

Majiya daga jami'an tsaro wacce ta bukaci a boye sunanta tace, abin ya bada mamaki ta yadda tsohon gwamnan ya shigo da makamai masu yawa haka kuma ba a ganoshi ba.

Jami'an tsaro sun bayyana damuwarsu gudun ko ba su kenan makaman da gwamnan ya shigo dasu kasar ba ba tare da izini ba.

Bayan fallasuwar lamari a watan Yuni, Amosun ya wallafa dogon rubutu da ke musanta laifinsa a shafinsa na tuwita don gudun kamashi.

Ga abinda ya wallafa: "Labarin da Premium Times ta wallafa gaskiya ne akan zargin mika makamai masu tarin yawa da mukayi ga gwamnatin tarayya." Daga nan yayi ikirarin ya samu amincewa daga ofishin mai bada shawara akan tsaro na tarayya da kuma ma'aikatar kudi ta tarayya don shigo da makaman a 2012.

Ya bayyana cewa, ya shigo da motocin yaki 13, bindigogi kirar AK47 1,000, alburusai miliyan biyu, rigunan da alburushi baya fasawa 1,000, hulunan karfe 500 da sauransu a 2012.

Yace an shigo da kayan yakin ne don karfafa 'yan sandan jihar Ogun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel