Likitocin jahar Kaduna za su tsunduma yajin aiki saboda rashin jituwa da gwamnati

Likitocin jahar Kaduna za su tsunduma yajin aiki saboda rashin jituwa da gwamnati

Kungiyar likitoci ta Association of Resident Doctors, reshen jahar Kaduna ta baiwa gwamnatin jahar Kaduna wa’adin kwanaki 21 domin shiga yajin aiki matukar bata cika mata yarjejeniyar da suka shiga shekaru 2 da suka gabata ba.

Shugaban kungiyar, Emmanuel Joseph ya bayyana haka yayin wata ganawa da ya yi da manema labaru a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba a garin Kaduna, yace a ranar Laraba suka aika ma gwamnati da wannan gargadi.

KU KARANTA: Wani mutum mai yara 23 ya yi cinikin dansa a kan kudi naira miliyan 5 a Nassarawa

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Emmanuel yace za su koma gidan jiya na yajin aikin da suka fara matukar gwamnati bata cika alkawurran da ta daukan musu ba zuwa karshen wa’adin kwanaki 21.

“Mun rattafa hannu a kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninmu da gwamnati a kan yadda za’a magance matsalar a shekaru biyu da suka gabata, wanda hakan ne yasa muka janye yajin aikin da muka shiga.

“Tun daga wancan lokaci mun yi ta kokarin janyo hankalin gwamnati ga wannan yarjejeniya domin ta aiwatar dasu kamar yadda ta yi alkawari, kwatsam sai a ranar 27 ga watan Satumbar 2019 muka samu wata takarda daga gwamnati.

“Abubuwan da wannan takarda ta kunsa sun saba ma yarjejeniyar da muka shiga da gwamnati, asali ma gwamnati na neman ta rage albashi da alawus alawus na likitoci da kashi 24-49 a kowanni matakin aiki.

“Daga cikin bukatunmu guda 8 dake cikin yajejeniyar da muka rattafa ma hannu, bukatu 2 kacal gwamnati ta yi kokarin biya mana, suma ba gaba daya ba, bayan kwashe shekaru 2 ana abu daya.” Inji shi.

Don haka Emmanuel yace yana fatan gwamnati za ta dauki wa’adin kwanaki 21 da kungiyars ta bata da muhimmanci, domin ta gyara matsalolin dake kunshe a cikin sabuwar takardar da ta aiko mata, tare da tabbatar da cika alkawurran da ta dauka a cikin yarjejeniyar da suka cimma shekaru 2 da suka gabata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel