Annobar cutar shawara ta kashe mutane 29, ta kama 224 a jahar Bauchi

Annobar cutar shawara ta kashe mutane 29, ta kama 224 a jahar Bauchi

Shugaban hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko, BSPHDA, Rilwanu Mohammed ya bayyana cewa akalla mutane 224 suka kamu da barkewar cutar shawara da ta mamaye wasu sassan jahar, tare da kashe mutane 29 daga cikinsu.

Rahoton jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Rilwanu ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Alhamis a garin Bauchi, inda yace a garin Alkaleri aka fara samun bullar cutar.

KU KARANTA: Wani mutum mai yara 23 ya yi cinikin dansa a kan kudi naira miliyan 5 a Nassarawa

“Mun samu mutane 224 da suka kamu da cutar, yayin da mutane 29 daga cikinsu suka mutu. A karamar hukumar Alkaleri kadai akwai mutane 24 da suka mutu, sai mutane 2 a karamar hukumar Bauchi, 1 a Darazo da kutame 2 a karamar hukumar Ningi.” Inji shi.

Shugaban hukumar ya kara da cewa an fara samun bullar cutar ne a karamar hukumar Alkaleri tun a watan Satumba, amma a yanzu sun dage matuka domin dakile yaduwar cutar zuwa wasu sassan jahar.

“Da wannan ne gwamnati ta fara kaimi wajen dakatar da wanzuar cutar ta hanyar yin allurar rigakafi ga mutanen dake zaune a garuruwan da cutar ke barazana. Zuwa yanzu an gudanar da allurar rigakafi gua 500,000 a Alkaleri, kuma muna sa ran yin allura 600,000 a Ningi.” Inji shi.

Sai dai duk da cewa shugaba Rilwanu ya bayyana cewa ba’a daukan cutar shawara, amma yana iya yaduwa ta hanyar cizon sauro, don haka ya nemi jama’a su tabbata sun sanar da hukuma da zarar sun fara ganin abubuwan da basu gane ba a yankunansu.

Sa’annan daga karshe ya yi kira ga jama’a da su rungumi allurar rigakafin tare da amincewa da shi, saboda ta haka ne kadai za’a iya kawar da cutar daga jahar Bauchi gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel