Wani mutum mai yara 23 ya yi cinikin dansa a kan kudi naira miliyan 5 a Nassarawa

Wani mutum mai yara 23 ya yi cinikin dansa a kan kudi naira miliyan 5 a Nassarawa

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, NSCDC ta sanar da kama wani mutumi dan shekara 42 dake mata 5, da y’ay’a 23 da laifin sayar dsa wani karamin dansa mai shekaru 3 a kan kudi naira miliyan 5 a jahar Nassarawa.

Jaridar The Nation ta ruwaito kwamandan NSCDC reshen jahar Nassarawa, Mohammed Mahmoud Fari ne ya bayyana haka ga manema labaru a ranar Alhamis a garin Lafiya, inda yace sun kama mutumin ne a ranar Talata.

KU KARANTA: Masu tsaron Osinbajo sun casa wani dan jarida yana kallo babu abin da ya yi

Kwamandan yace shi dai wannan mutumi dan asalin karamar hukumar Obi ne, kuma ya kammala shirye shiryen sayar da dansa a kan kudi naira miliyan 5 a lokacin da jami’an hukumar suka samu labari, sai suka yi basaja a matsayin su zasu siya yaron, amma yace kudi hannu za’a bashi, a haka suka kama shi.

Binciken hukumar ya nuna cewa mutumin da ba’a bayyana sunansa ba yana da mata 5, da yara 23, kuma bincike ya tabbatar da cewa ya taba sayar da wata diyarsa mace guda daya, kamar yadda kwamandan ya tabbatar.

Sai dai mutumin ya amsa laifinsa, amma ya danganta hakan ga talauci da matsanancin hali da ya tsinci kansa a ciki, inda yace ya yanke shawarar sayar da dan nasa ne saboda ya samu kudin da zai kula da sauran iyalinsa.

A hannu guda kuma, kwamanda Mohammed ya bayyana wani mutumi dan shekara 45 da jami’an hukumar NSCDC suka kama shi da laifin yi ma diyar makwabcinsa yar shekara 10 fyade a titin Almakura dake garin Lafiya.

Daga karshe kwamandan yace da zarar sun kammala gudanar da bincike a kan mutanen za su gurfanar dasu gaban kuliya manta sabo domin samun hukuncin da ya yi daidai da laifukan da suka tafka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel