Yan Najeriya sun yi zanga zanga a Birtaniya saboda ziyarar Buhari kasar

Yan Najeriya sun yi zanga zanga a Birtaniya saboda ziyarar Buhari kasar

Yan Najeriya mazauna kasar Birtaniya sun gudanar da zanga zangar nuna adawa da ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai kasar Birtaniya inda yace zai huta na tsawon kwanaki 15 a gidan gwamnatin Najeriya dake Ingila.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito yan Najeriyan sun gudanar da zanga zangar ce a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba a karkashin jagorancin Gabriel Agbontaen na kungiyar Global Coalition for Security and Democracy in Nigeria, a gaban Abuja House inda Buhari ke zaune.

KU KARANTA: Masu tsaron Osinbajo sun casa wani dan jarida yana kallo babu abin da ya yi

Masu zanga zangar sun yi zargi Buhari da zuwa neman lafiya a kasar Birtaniya, don haka suka nemi ya koma gida Najeiya ya gyara asibitocin kasar a maimakon yawon duniya yana neman lafiya, da kuma shirin dauko hayan likitocin kasashen waje zuwa Najeriya.

Haka zalika sun bayyana rashin ababen more rayuwa da matsalar tsaro a matsayin abubuwan dake sanya shuwagabannin Najeriya zuwa yawo kasashen waje, don haka suka caccaki shugaba Buhari kan yadda yake amfani da ababen more rayuwa a kasashen waje, alhali ya haramta shigar da shinkafar kasar waje Najeriya.

Rahotanni sun tabbatar da shugaba Buhari ya kwashe tsawon kwanaki 409 a kasashen waje, daga cikinsu ya kwashe sama da kwanaki 200 wajen neman lafiyarsa a kasar Birtaniya. Bugu da kari masu zanga zangar sun ce tunda dai Buhari ya yi ikirarin ziyarar kashin kai ya kai Birtaniya, bai kamata ya yi amfani da kudaden gwamnati ba.

Majiyarmu ta cigaba da cewa daga lokacin da Buhari ya hau karagar mulki a shekarar 2015, an yi ma asibitin fadar shugaban kasa na Aso Rock Villa kasafin kudi daya haura naira biliyan 10, amma ko a shekarar 2017 sai da aka jiyo uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari tana kokawa a kan rashin kayan aiki a asibitin, hatta sirinjin allura.

Daga karshe dai babu wanda ya fito daga Abuja House don ya gana da masu zanga zangar, amma an hangi wasu mutane daga cikin gidan suna daukan masu zanga zangar bidiyo da wayoyi, haka zalika an girke Yansandan Birtaniya domin su tabbatar da tsaro.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel