Korar hadiman Osinbajo 35: Kakakin mataimakin shugaban kasa ya karyata batun

Korar hadiman Osinbajo 35: Kakakin mataimakin shugaban kasa ya karyata batun

- Mai magana da yawun mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya karyata rahotannin da jaridu da dama suka wallafa na korar hadiman mai gidansa 35

- Rahotannin da suka karade shafukan sada zumunta da labarai sun ce shugaba Muhammadu Buhari ya sallami hadiman Osinbajo 35 kana an kwace takardar shaidar shiga Aso Villa daga hannunsu

- Sai dai kakakin na Osinbajo, Laola Akande ya ce labarin kanzon kurege ne kawai amma ya nemi afuwar wani dan jaridar fadar shugaban kasa da jami'an tsaro suka duka kuma ya ce anyi sulhu

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Laolu Akande ya ce ya nemi afuwar Mista Abayomi Adeshida, dan jaridar kamfanin Vanguard da ke daukan rahoto a gidan gwamnati da ke birnin tarayya Abuja da jami'an tsaro suka lakadawa duka a safiyar ranar Alhamis.

A sakon da Laolu ya wallafa a shafinsa ta Twitter, ya ce anyi nadamar afkuwar lamarin.

Ya kuma kara da cewa jerin sunayen da ke yawa a kafafen labarai da sunan cewa hadiman mataimakin shugaban kasar ne da aka sallama ba gaskiya bane kuma ya bukaci al'umma suyi watsi da shi.

DUBA WANNAN: Ire-iren abinci 5 da ya kamata dan adam ya guda kafin kwanciya barci

Laolu ya rubuta, "An warware matsalar da ta janyo rikici tsakanin jami'in tsaro da dan jarida mai daukan hoto a fadar shugaban kasa, Mista Adeshida da ya faru a yau Alhamis. Ba mu ji dadin afkuwar lamarin ba kuma na nemi afuwarsa kan keta masa hakki da aka yi. Kazalika, jerin sunayen wasu hadiman fadar shugaban kasa da aka ce wai an kora karya ne kuma ya kamata al’umma suyi watsi da shi."

A baya-bayan nan dai ana ta hasashen cewa akwai rashin jituwa tsakanin mataimakin shugaban kasar da mai gidansa Shugaba Muhammadu Buhari duba da cewa shugaban kasar ya kwace wasu hukumomi da ke karkashin ofishinsa a kwanakin baya.

Sai dai fadar ta shugaban kasa ta musanta batun inda ta ce har yanzu shugaban kasar da mataimakinsa suna girmama juna kuma kansu bai rabu ba kawai dai ana yin wasu canje-canje ne don inganta ayyukan gwamnatin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel