Sallaman hadiman Osinbajo 35, babban hadimin shugaban kasa ya yi tsokaci

Sallaman hadiman Osinbajo 35, babban hadimin shugaban kasa ya yi tsokaci

Babban hadimin shugaban kasa kan shirye-shiryen jin dadin al'umma, Barista Isma'eel Ahmad, ya tofa albarkacin bakinsa kan sallamar hadiman mataimakin shugaban kasa 35 da ake rade-radin cewa shugaba Buhari ya sallama.

A wata hira na musamman da Legit.ng Hausa tayi da shi, Barista Isma'il ya bayyana cewa ai ba wani abu bane idan shugaban kasa ya yanke shawarar sallamarsu tunda shine ya nada su.

Yace: "Dama shi daukesu aiki, ai Buhari ne ke daukan aiki, kuma hadiman ai ba nasa bane,na Buhari ne.

Babu wanda yayi laifi, gani akayi ya kamata ayi hakan kuma wasu an turasu ma'aikatu daban-daban suna aiki. Wannan ba wani abu bane, rayuwa ce ta gwamnati kowa ya saba."

Sallaman hadiman Osinbajo 35, babban hadimin shugaban kasa ya yi tsokaci

Sallaman hadiman Osinbajo 35, babban hadimin shugaban kasa ya yi tsokaci
Source: Original

Da wakilin Legit a tambayesa meyasa aka yi hakan lokacin da ake rade-radin takun saka tsakanin Buhari da mataimakinsa, Barista Ahmad yace:

"Ai bikin Magaji bai hana na magajiya, don mutane na zargi-zargi ana hasashe-hasashe sai a ce ba za'ayi aikin gwamnati ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel