Kungiyar Boko Haram ta kai wa sojojin Najeriya farmaki, ta kashe mutum 10

Kungiyar Boko Haram ta kai wa sojojin Najeriya farmaki, ta kashe mutum 10

- Kungiyar yan ta’addan Boko Haram sun kai harin bazata kan sojojin Najeriya a yankin Domboa da ke jihar Borno a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba

- An tattaro cewa sojoji 10 sun rasa ransu yayinda wasu 12 suka bata sannan tara suka jikkata

- Har ila yau majiyar soji ta bayyana cewa sun yi nasarar kashe yan ta'addan tara bayan sun yi arangama

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa yan ta’addan Boko Haram sun kai harin bazata kan sojojin Najeriya a yankin Domboa da ke jihar Borno a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba, inda hakan ya yi sanadiyar mutuwar dakarun soji 10.

Wata majiyar soji da ta nemi a sakaya sunanta a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba, ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa sojoji 12 sun bata bayan harin

Ta ce: "Mun rasa sojoji 10 a lokacin wani arangama da 'yan ta'adda da suka yi wa sojojinmu na bazata yayin wani sintiri a yankin," cewar majiyar.

"Sojoji tara sun jikkata sannan muna neman 12."

Sojojin dai sun fuskanci harin 'yan kungiyar ne lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa sansaninsu da ke Damboa mai nisan kilomita 88 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

Wata majiyar ta soji ta kara da cewa arangaman ya tilasta wa sojojin tserewa duk da cewa sun sami nasarar kisan 'yan kungiyar ta’addan tara.

KU KARANTA KUMA: Wata kungiya ta caccaki Buhari a kan rashin damka kasa a hannun Osinbajo kafin ya yi bulaguro

'Yan kungiyar sun kuma kone motocin sojoji sannan kuma sun yi awon gaba da mota kirar a kori-kura da kuma wasu bindigogi shida.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Ministar taimakon jama'a da kiyaye afkuwar annoba, Sadiya Umar Farouq, ta dora alhakin rashin karewar rikicin Boko Haram a kan rashin kyawawan dabaru da kulla alaka mai kyau bangaren rundunar soji da sauran kungiyoyi masu zaman kansu da ke yankin arewa maso gabas.

Uwargida Sadiya ta bayyana hakan ne a wurin bude wani taro na kwanaki uku na hadin gwuiwa da jami'an tsaro da aka fara a ranar Alhamis a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel