An yi artabu tsakanin Jami'an tsaro da yan Boko Haram da sukayi kokarin afkawa Damaturu

An yi artabu tsakanin Jami'an tsaro da yan Boko Haram da sukayi kokarin afkawa Damaturu

Wasu yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun yi kokarin fasa cikin garin Damaturu, babbar birnin jihar Yobe, kwamishanan yan sandan jihar, Yahaya Abubakar, ya tabbarwa manema labarai ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa jami'an tsaro sun kawar yan ta'addan sakamakon rahoton leken asirin da suka samu kan motsin yan ta'addan cikin garin.

CP Abubakar ya ce gamayyar jami'an tsaro na yan sanda da Sojoji da taimakon jiragen yaki biyu da suka dira inda suke da wuri kuma aka samu nasara. Channels TV ta ruwaito.

Ya kara da cewa babu wanda aka rasa a bangaren jami'an tsaro.

Kwamishanan yace: "Al'ummar garin Mafa ne suka bayyana mana tafiyarsu"

"Jami'an tsaro (Soji da yan sanda); mun hada kai kuma mun samu nasarar kawar da harin. Yanzu komai na lafiya."

KU KARANTA:

Hakazalika Kakakin rundunar 27 Task Force Brigade, Kyaftan Njoka Irabor, ya tabbatar da hakan.

A bangare guda, Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa kowa ya san inda mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suke zama, don haka abin da kawai ya rage shi ne a far musu.

Zulum ya bayyana haka ne a ranar Talata, 5 ga watan Nuwamba a yayin wani babban taron tsaro da babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammad Adamu ta shirya a jahar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel