An kwace shaidar shiga fadar shugaban kasa daga hannun hadimai 35 na Osinbajo

An kwace shaidar shiga fadar shugaban kasa daga hannun hadimai 35 na Osinbajo

A yau ne aka kwace shaidar shiga fadar shugaban kasa daga hannun hadimai 35 na Osinbajo da aka sallama. Wasikun sallamar aiki na hadimai 35 na ofishin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo sun kammala kuma sakatare gwamnatin tarayya, Boss Mustapha yasa hannu kuma ya mikasu ga ofishin mataimakin shugaban kasar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito yadda shugaban kasa Muhammadu buhari ya sallami hadiman mataimakin nasa 35 daga cikin 80.

Majiya mai karfi tace, sakataren gidan gwamnatin wanda yasa hannu a wasikun daukar hadiman aiki ne aka ba umarnin bawa wasikun sallamar tasu.

DUBA WANNAN: Ministan Buhari ya fadi abinda ya hana rikicin Boko Haram kare wa

Yayin tabbatar da isar wasikun sallamr ga ofishin mataimakin shugabn kasar, majiya ta sanar da jaridar Daily Nigerian cewa, mataimakin shugaban kasar ya rike wasikun har zuwa dawowar shugaban kasar daga birnin Landan don ya rokeshi.

A taron gaggawa da mataimakin shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin, Ade Ipaye, ya kira wadanda abin ya shafa, ya sanar dasu matsayar mataimakin shugaban kasar akan kokarinsa na ganin ya roki shugaban kasar don ya janye hukuncinsa.

Ana tsammanin dawowar shugaban kasar a ranar 17 ga watan Nuwamba.

Karfin ikon mataimakin shugaban kasar na disashewa a hankali sakamakon maida wasu cibiyoyin gwamnatin da yake lura dasu zuwa ofishin shugaban kasa ko kumama'aikatar da ta jibanceta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel