Wata kungiya ta caccaki Buhari a kan rashin damka kasa a hannun Osinbajo kafin ya yi bulaguro

Wata kungiya ta caccaki Buhari a kan rashin damka kasa a hannun Osinbajo kafin ya yi bulaguro

- Wata kungiyar Niger Delta, PANDEF, ta bayyana cewa baya bisa ka'ida ace Buhari ya yi tafiya batare da neman Osinbajo ya cigaba da mulki ba

- Olorogun Oyibode, wanda ya kasance shugaban kungiyar na kasa, ya bayyana cewa kundin tsarin mulki ta ba Osinbajo damar aiki a matsayin mukaddashin shugaban kasa idan shugaban kasar ya yi bulaguro

- Oyibode ya zargi yan hana ruwa gudu da haifar da rudani a fadar shugaban kasa

Shugaban kungiyar matasan PANDEF na kasa, Olorogun Vincent Oyibode, a jiya Laraba, 6 ga watan Nuwamba, ya ce karara ya saba Ma kundin tsarin mulki tafiya hutu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, ba tare da ya mika wa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo rikon kwarya ba.

Oyibode ya bayyana wa majiyarmu ta Vanguard cewa: “Wannan ya saba kundin tsarin mulki, doka a bayyane take karara kan lamarin hutun Shugaban kasar, koda kuwa na mako guda ne, kamata ya yi mataimakin Shugaban kasa ya cigaba da gudanar da lamura a matsayin mukaddashin shugaban kasa."

Jigon PANDEF din wanda ya yi maganan ne a daidai lokacin da ake tsaka da zargin sallamar hadiman Osinbajo 35 da Buhari ya yi, ya ce: “gwamnatin APC mai mulki cike take da abubuwan saba doka, masu hana ruwa gudu na kara ingiza rashin bin ka’ida ba tare da la’akari da abunda matakinsu zai haifar ga kasar ba.

“Wadanan masu hana ruwa gudu sune ke ingiza rashin bin ka’ida a hukumar cigaban Niger Delta ta hanyar kafa kwamitin wucin gadi wanda dokar hukumar bata san da su ba.

KU KARANTA KUMA: Masu tsaron Osinbajo sun casa wani dan jarida yana kallo babu abin da ya yi

“Kan lamarin sallamar wasu hadiman mataimakin Shugaban kasa, babu mamaki shugaba Buhari bai da masaniya a kan koran hadinan matainakin nasa,” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel