Martani: 'Yan majalisa sun kalubalanci Fashola akan maganar tituna

Martani: 'Yan majalisa sun kalubalanci Fashola akan maganar tituna

Ikirarin da ministan Buhari yayi na cewa titunan kasar nan basa cikin wani hali ya jawo cece-kuce a fadin kasar nan. Ba fadin kasar nan ba kadai, hatta 'yan majalisar wakilai sun maida martani akan ikirarin.

Mr Salam, dan majalisar wakilai ya kalubalanci ministan aiyukan da gidaje da sauran masu ruwa da tsaki da su yanke tafiye-tafiye a jirgin sama na watanni uku. Su koma amfani da titunan da suka ce ana zuzuta lalacewarsu ne. Ta hakan kawai ne zasu gane yawan lalatattun titunan kasar nan.

A ranar Laraba ne ministan aiyuka da gidaje na kasar nan, Babatunde Fashola, yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya, yace , titunan kasar nan basu yi lalacewar da ake ta zuzutawa ba.

Amma kuma dan majlisar wakilai Mr Salami, a ranar Alhamis ya kalubalanci ministan akan zancensa.

DUBA WANNAN: Titunan Najeriya basa cikin mummunan hali, in ji ministan Buhari

"Daga wannann kalamin da ministan yayi na gano cewa, wasu daga cikinmu da ke kujerun mulki har yanzu bamu san halin da 'yan kasar nan ke ciki ba. Ministan ya fadi irin wannan kalamin har sau biyu zuwa uku." cewar dan majalisar.

"Domin ganin halin da 'yan Najeriya ke ciki akan miyagun titunan kasar nan, akwai bukatar wadanda ke wakiltar mutane da su zagaya kasar amma ba a jirgi ba don ganin irin halin da 'yan kasar ke ciki a koda yaushe." in ji dan majalisar.

Dan majalisar wakilan yace "Sai lokacin da ministan tare da sauraan amsu ruwa da tsaki ne suka ga halin da titunan kasar nan ke ciki na dan tsawon lokaci, toh zasu fahimci abinda 'yan Najeriya ke ta zuzutawa. A matsayina na dan majalisar da ke kwamitin aiyuka, ina kalubalantar ministan aiyuka da wadanda abin ya shafa dasu yi yawo a titunan kasar nan na kwanaki 90,"

"Idan kuwa muka karbi wannan kalubale, akwai yuwuwar mu dawo tare da yin duk abubuwan da zasu tseratar da tattalin arzikinmu sakamakon halin da titunan ke ciki," in ji shi

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel