Gwamnatin jihar Barno ta fadi kudi mai tsoka da za ta dinga biyan 'yan bautar kasa

Gwamnatin jihar Barno ta fadi kudi mai tsoka da za ta dinga biyan 'yan bautar kasa

- Gwamnatin jihar Barno a ranar Alhamis tayi kira ga masu hidimar kasa da su garzayo jihar don kwasar sha tara ta arziki da gwamnatin jihar ta tanadar

- Gwamnatin jihar tayi alkawarin biyan duk mai bautar kasa N10,000 a duk wata

- Ta kara da cewa, akwai tabbacin tsaro ga rayukansu da dukiyoyinsu da gwamnatin jihar ke da shi

Gwamnatin jihar Barno a ranar Alhamis ta sanar da cewa zata dinga ba wa duk dan hidimar kasa N10,000 a duk wata.

Yayin rantsar da masu bautar kasa na jihar dake sansanin bautar kasa na jihar Katsina, shugaban hukumar NYSC na jihar, Dr Sambo Barka Amaza, yace , a watan da ya gabata kadai gwamnatin jihar Barno ta kashe naira miliyan 87 a matsayin alawus din masu hidimar kasa a jihar..

Kamar yadda yace, duk likitocin da aka tura ma'aikatu, bangarori da cibiyoyin lafiya na jihar za a dinga biyansu N100,000 inda sauran malaman jinya zasu dinga karbar N50,000 a duk wata. Za a kuma bawa masu bautar kasar gurin kwana mai kyau a duk fadin jihar.

DUBA WANNAN: Titunan Najeriya basa cikin mummunan hali, in ji ministan Buhari

Yace "Gwamnatin jihar na hada kai da jami'an tsaro a fadin jihar don tabbatar da tsaron rayuka da kadarorin masu hidimtawa kasar."

"Ina kira gareku da ku garzayo jihar Barno don hidimtawa kasarku. Ina tabbatar muku da cewa, rayukanku da kadarorinku na tsare ba kamar yadda kafafen yada labarai ke sanarwa ba. Har a yau jihar Barno tana nan a gidan zaman lafiya," ya kara da cewa.

Tun a farko, mashiryin NYSC na jihar, Rabiu Aminu, ya hori masu hidimar kasar da su kasance masu ladabi da jajircewa. Ya kara da cewa, masu hidimar kasa su guji kungiyoyin asiri da sauran lamurran rashin gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel