Yanzu - yanzu: Kotu ta jaddada nasarar wani sanatan APC

Yanzu - yanzu: Kotu ta jaddada nasarar wani sanatan APC

- Kotun daukaka kara da ke Owerri ta jaddada nasarar Sanata Rochas Okorocha a zaben 23 ga watan Fabrairu da ya gabata

- Kotun ta ce hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe yayi dai-dai

- Masu karar sun kasa bayyana gamsassun shaidu akan magudi da canza sakamakon zabe da jami'in bayyana sakamakon zaben yace yayi karkashin barazana

Kotun daukaka kara da ke Owerri a ranar Alhamis ta jaddada nasarar Sanata Rochas Okorocha, a zaben sanata mai wakiltar mazabar Imo ta yamma da ta gabata.

Shugaban kungiyar alkalan, R. A Ada, wanda ya karanto hukuncin, yace daukaka karar da Osita Izunaso na jam'iyyar APGA da Jones Onyereri na jam'iyyar PDP suka yi ta kalubalantar nasarar Sanata Okorocha bata da makama.

DUBA WANNAN: Yanzu -Yanzu: Pantami dakatar da biyan tsabar kudi a ofisoshin NIPOST

Alkalin ya tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben akan shari'ar Okorocha din. Yace shari'ar bata da matsala kuma kotun daukaka kara ta yarda da ita.

Kungiyar alkalan tace, karar ta kasa bayyana gamsassun shaidu akan zargin magudi, cika kuri'u, canza sakamakon zabe da kuma kwace sakamakon daga hannun ma'aikatan zaben.

Mai shari'ar yace, karar ta kasa bada shaidu akan barazanar da aka yiwa jami'in INEC mai bayyana sakamakon zaben har ya sanar cewa Okorocha ne ya lashe zaben.

A ranar 23 ga watan Fabrairu ne Okorocha ya kada Onyereri da Izunaso amma sai jami'in da ya sanar da sakamakon zaben yace anyi mishi barazana ne sannan ya sanar da sakamakon zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel