Masu tsaron Osinbajo sun casa wani dan jarida yana kallo babu abin da ya yi

Masu tsaron Osinbajo sun casa wani dan jarida yana kallo babu abin da ya yi

A yau ne wasu jami’an tsaro dake gadin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo suka sauke fushinsu a kan wani dan jarida mai daukan hoto dake aiki da gidan jaridar Vanguard, inda suka lakada masa dan banzan duka.

Jaridar The Cable ta ruwaito lamarin ya faru ne a cikin fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa, yayin da Osinbajo ya halarci taron hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje daya gudana a babban dakin taro na Villa.

KU KARANTA: An bankado cikakken sunayen hadimai 35 da Buhari ya fatattaka daga ofishin Osinbajo

A wannan lokaci ne dan jaridar mai suna Adeshida Abayomi ya tsaya yana daukan mataimakin shugaban hotuna, kwatsam sai ya ga jami’an hukumar tsaro na DSS sun far masa, suka shiga dukansa, suna jan shi a kasa, tare da farfasa masa na’urar daukan hotonsa.

Duk wannan lamari ya faru ne a gaban mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, amma ko uffan bai ce ba, babu abin da ya yi domin ya hanasu, sai dai babban dogarinsa ne ya sa baki suka kyale ni.

“Na yi mamaki a lokacin da jami’an DSS suka diran min da duka babu gaira babu dalili. Suka kekketa shaidar izinin shigata Villa, suka dinga ja na a kasa yayin da suka jibgata, suna harbi na da kafafuwansu. A yanzu haka duk jikina ciwo yake, musamman kafata ta dama.

“Basu daina dukana ba har sai da babban dogarin mataimakin shugaban kasa yasa baki, wanda na yana nuna musu da hannu a kan su kyale ni.” Inji shi.

Duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin kaakakin Osinbajo, Laolu Akande, amma hakan ya ci tura.

A wani labari kuma, an samo cikakken jerin sunayen hadiman mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallama daga aiki, tare da mukamansu.

Daga cikin su akwai Ajibola Ajayi, diyar tsohon gwamnan jahar Oyo, Isiaka Abiola Ajimobi wanda it ace hadimar Osinbajo ta musamman a kan harkar shari’a, Lanre Osinbona, babban mataimaki na musamman a kan sadarwar zamani, Imeh Okon babban mataimaki na musamman a kan manyan ayyuka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel