Yanzu-yanzu: Saura kirin APC ta sake rashi, bulaliyar majalisa ya samu nasara a kotun Afil

Yanzu-yanzu: Saura kirin APC ta sake rashi, bulaliyar majalisa ya samu nasara a kotun Afil

- Bulaliyar majalisa Orji Kalu ya tsallake rijiya da baya a kotu

- Jam'iyyar APC ta rasa akalla kujeru hudu a majalisar dattawa cikin makon nan

Bayan rashin manyan yan jam'iyya a biyu majalisar wakilai da kuma biyu a majalisar dattawa da APC tayi a farkon makon nan, ta samu gagarumin nasara a kotu daukaka kara a majalisar dattawa a yau.

Bulaliyar majalisa, Orji Uzor Kalu, ya samu nasara a kotun daukaka kara inda ta tabbatar da shi matsayin sahihin wanda ya lashe zaben kujeran Sanata mai wakiltar jihar Abiya ta Arewa.

Orji Kalu ya bayyana godiyarsa ga Allah kan wannan nasara da ya samu a kotun.

Yace: "Mun samu nasara a kotun daukaka kara yau. Bani wani abin cewa Illa mika godiya ga Ubangiji tare da godewa dukkan magoya bayanmu na jajircewan da sukayi a wannan tafiya."

A bangare guda, hukumar zabe mai zaman kanta da ta dawo da Misis Natasha Akpoti ta jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a matsayin yar takara a zaben gwamna da za a yi a jihar Kogi a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Justis Folashade Ogunbanjo-Giwa ta babbar kotun tarayya Abuja ce ta bayar da umurnin a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba.

Ta bayyana cewa INEC ta yi gaban kanta ta hanyar kin amincewa da jam’iyyar da yar takararta a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel