An dakatar da shari’ar Maina sai Nuwamba 21 domin duba gaskiyar rashin lafiyarsa

An dakatar da shari’ar Maina sai Nuwamba 21 domin duba gaskiyar rashin lafiyarsa

Babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ya dakatar da shari’ar da ake yi da tsohon shugaban kwamitin gyaran harkar fansho na Najeriya, Mista Abdulrasheed Maina sai nan da makonni biyu.

Kamar yadda Channels TV ta kawo rahoto, za a koma zama a kotu ne a Ranar 21 da 22 ga Watan Nuwamba. Alkalin kotu ta dauki wannan hukunci ne a zaman da aka yi Ranar 7 ga Nuwamba.

A zaman yau Alhamis. Alkali mai shari’a ya dauki matakin dage karar har sai bayan kwanaki goma sha hudu. Lauyan wanda ake tuhuma, Adedoye Adedipe, ya nuna cewa sam ba su da ja.

Lauyoyin gwamnati da ke karar Abdulrasheed Maina ne su ka bukaci Alkali ya dage shari’ar. A wata takarda, masu karar sun ce za a bukaci kusan mako guda domin a binciki ainihin lafiyarsa.

"Tun da Aminina wanda ya tsayawa masu tuhuma ba Likita ba ne, zai zama shiga sharo-ba shanu a ce ya bukaci a cigaba da shari’a bayan ba a kawo kotun takardun lafiyarsa ba." Inji takardar.

KU KARANTA: Kotu ta sake ba Gwamnan Kaduna gaskiya a shari'ar 2019

M.S Abubakar wanda ya tsayawa masu kara ya ce ba a yi wa kasa adalci ba idan aka yi haka, inda ya nemi a cigaba da gudanar da shari’a tun da har shaidan masu kara na farko ya hallara a kotu.

Rahoton ya ce Lauya Abubakar ya fadawa Alkali mai shari’a cewa shawara kurum ya bada na cewa a saki wanda ake zargin a kan beli saboda halin rashin lafiyarsa kamar yadda ya ke ikirari.

Bayan sauraron karar, Okon Abang ya ce ya amince za a sake zama a Ranar 21 na Nuwamba kamar yadda aka bukata. Alkalin ya ce halin da ya ga wanda ake zargi ya ba shi tausayi matuka.

Ganin an kawo Abdulrasheed Maina kotu a kan keken guragu ya sa Mai shari’a Okon Abang ya dakatar da zaman. Ana zargin Maina ne da laifin awon gaba da Biliyan 2 lokacin da ya ke ofis.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel