Yan kwanaki kafin zabe: Kotu ta umurci INEC da ta dawo da yar takarar SDP a zaben gwamnan Kogi

Yan kwanaki kafin zabe: Kotu ta umurci INEC da ta dawo da yar takarar SDP a zaben gwamnan Kogi

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an bukaci hukumar zabe mai zaman kanta da ta dawo da Misis Natasha Akpoti ta jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a matsayin yar takara a zaben gwamna da za a yi a jihar Kogi a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Justis Folashade Ogunbanjo-Giwa ta babbar kotun tarayya Abuja ce ta bayar da umurnin a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba.

Ta bayyana cewa INEC ta yi gaban kanta ta hanyar kin amincewa da jam’iyyar da yar takararta a zaben.

Ta kara da cewa hukumar ba ta da ikon hana kowani dan takara yin takara a wani zabe ba tare da goyon bayan kotu ba.

Sannan ta kuma umurci hukumar da ta sanya alamar SDP a takardar kada kuri’a da za a yi amfani dashi a zaben.

KU KARATA KUMA: Zargin cin amanar kasa: DSS ta karyata batun kin sakin Sowore

A wani labarin kuma, mun ji cewa jam’iyyar hamayya ta PDP ta zargi mai girma gwamnan jihar Kogi da kuma Darektan yakin neman zabensa watau Sanata Smart Adeyemi da yunkurin cafke Sanata Dino Melaye.

PDP ta ce gwamnan mai neman tazarce da kuma Smart Adeyemi su na kitsa hanyar da za su bi su cafke Dino Melaye, su garkame shi kafin zaben da za ayi Ranar 16 ga Watan Nuwamban nan.

Jam’iyyar ta ce Jagororin na APC sun kitsa wannan ne a wani taro da su ka yi a gidan gwamnatin jihar Kogi. Wani Hadimin Sanata Dino ne Melaye mai suna Mista Gideon Ayodele, ya bayyana wannan.

A Ranar Talata, 5 ga Watan Nuwamban 2019, Gideon Ayodele ya fitar da jawabi ya na zargin gwammatin jam'iyyar APC da kuma Sarkin yakin gwamnan na jihar Kogi da shirya yadda za a kama Maigidansa yayinda ake shirin Zabe.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel