Kano: Kotun daukaka kara ta sa ranar fara sauraron shari'ar Abba gida-gida da Ganduje

Kano: Kotun daukaka kara ta sa ranar fara sauraron shari'ar Abba gida-gida da Ganduje

Kotun daukaka kara ta yankin jihar Kaduna, ta sa ranar Litinin, 11 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da zata saurara tare da jin karar zaben gwamnan jihar Kano tsakanin Injiniya Abba Kabir Yusuf da Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da jam'iyyar APC.

Kotun daukaka karar ta sanar da duk bangarorin shari'ar ne a yau ranar Alhamis.

Jaridar Solacebace ta ruwaito cewa, kotun daukaka karar na da daga nan har zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba don bayyana hukuncinta akan karar.

DUBA WANNAN: Yanzu - Yanzu: Maina ya bayyana a kotu kan keke guragu

Idan ba zamu manta ba, a ranar 2 ga watan Oktoba ne kotun sauraron kararrakin zabe dake Kano karkashin jagorancin Jastis Halima Shamaki ta kori karar Abba Kabir Yusuf da jam'iyyar PDP akan kalubalantar nasarar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Tuni kuwa mabiya darikar Gandujiyya suka dinga murna da farinciki. A daya bangaren kuwa na 'yan kwankwasiyya, hakan ya saka musu abin jimami da alhini.

Alkali Halima Shamaki ce ta karanto dalilan da yasa aka kori shari'ar tare da jaddada nasara Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sahihin mai kujerar.

A take lauyoyin jam'iyyar PDP suka bayyana cewa anyi hakan da manufa kuma ba zasu yi kasa a guiwa ba wajen daukaka kara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel