Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben El-Rufai

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben El-Rufai

- Kotun daukaka kara reshen Kaduna ta tabbatar da Malam Nasir Ahmad El-Rufai, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka yi a ranar 9 ga watan Maris, 2019 a jihar Kaduna

- Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Isah Ashiru ne suka daukaka kara a gaban kotun, inda suke kalubalantar hukuncin kotun zabe na jaddada zaben El-Rufai

- A halin yanzu, kwamitin mutum biyar na kotun daukaka karar a yau Alhamis ta tabbatar da hukuncin kotun zaben sannan ta kaddamar da El-Rufai a matsayin ainahin zababben gwamnan jihar

Kotun daukaka kara reshen Kaduna a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba, ta tabbatar da zaben Malam Nasir Ahmad El-Rufai, a matsayin gwamnan jihar Kaduna a zaben gwamna da aka yi a ranar 9 ga watan Maris, 2019.

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Isah Ashiru ne suka daukaka kara a gaban kotun, inda suke kalubalantar hukuncin kotun zabe, wacce ta kaddamar da El-Rufai a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zabe mai zaman kanta da fari ta kaddamar da El-Rufai a matsayin wanda ya lashe zaben.

Amma jam’iyyar PDP da dan takararta suka shigar da korafi gaban kotun zabe kan hujjar cewa anyi magudi sosai a zaben.

Sun bukaci kotun zaben da ta soke kuri’u 515,951, wanda suka yi ikirarin cewa an karawa APC ba bisa ka’ida bad a kuma kuri’u 124,210 da suka ce an karawa PDP, ta hanyar kuskure ko shigar da sakamakon sau biyu a takardar zabe wanda INEC ta yi.

A halin da ake ciki, kwamitin mutum biyar na kotun daukaka karar a ranar yau Alhamis ta tabbatar da hukuncin da kotun zaben ta yanke sannan ta kaddamar da Gwamna Ahmad Nasir El-Rufai a matsayin ainahin zababben gwamnan jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel