Zargin cin amanar kasa: DSS ta karyata batun kin sakin Sowore

Zargin cin amanar kasa: DSS ta karyata batun kin sakin Sowore

Hukumar tsaro na DSS a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba ta karyata rahotannin cewa ta ki ba umurnin kotu hadin kai wacce ta bukaci a bayar da belin jagoran zanga-zangar juyin-juya hali, Omoyele Sowore.

Sowore na fuskantar shari’a kan zargin cin amanar kasar.

Kakakin rundunar DSS, Peter Afunaya ya bayyana ma Channels Television cewa ba a sanar da hukumar cewa Sowore ya cika ka’idojin belinsa ba kamar yadda kotun ta yi hasashe.

Duk da cewar sun cika ka’idojin beli, Sowore, da abokin tafiyarsa, Olawale Bakare, na tsare a hannun hukumar DSS bayan Justis Ijeoma Ojukwu ta babbar kotun tarayya Abuja ta yi umurnin sakinsu a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba.

Lauyan Sowore, Mista Femi Falana, ya bayyana a ranar Laraba cewa wadanda ya ke karewa sun cika ka’idojin da aka sanya masu game da tuhumar da ake masu na cin amanar kasa.

Ya kara da cewa lauyoyi daga tawagarsa za su je ofishin DSS a safiyar ranar Alhamis domin ganin an saki wadanda suke karewa.

KU KARANTA KUMA: Wata uwa ta bayyana dalilinta na jefar da jinjirin da ta haifa a cikinta

A halin da ake ciki, Justis Ijeoma Ojukwu ta dage shari’an Sowore zuwa ranakun 5 da 6 ga watan Disamba, 2019.

A baya mun ji cewa kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umurnin sakin, Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar ADC a zaben Fabrairun 2019 kuma jagoran 'yan neman juyin juya hali wato #RevolutionNow kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A baya, lauyansa, Femi Falana (SAN) ya ce an cika dukkan ka'idojin bayar da belinsa da kotu ta gindaya.

Femi Falana ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba, inda yace Omoyele Sowore tare da abokinsa Olawale Bakare sun cika sharuddan beli a kan tuhume tuhumen cin amanar kasa da gwamnatin Najeriya ke musu kamar yadda Punch ta ruwaito.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel