Aikin jin kai: Aisha Buhari ta tallafa ma mata da matasa 600 a jahar Adamawa

Aikin jin kai: Aisha Buhari ta tallafa ma mata da matasa 600 a jahar Adamawa

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari ta bayar da tallafi ga mata da matasa 600 a jahar Adamawa a karkashin ayyukan gidauniyarta ta Future Assured Foundation, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyarmu ta ruwaito babban jami’in dake kula da ayyukan gidauniyar Future Assured, Alhaji Yau Babayi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba a birnin Yola, inda yace gidauniyar ta tsamo mutane 600 daga kananan hukumomin jahar 21 daga kangin talauci.

KU KARANTA: Halima Dangote da manyan daraktoci 5 sun ajiye aiki daga kamfanin Dangote

“A karkashin gidauniyar Future Assured mun horas da mata da matasa 600 a fannoni daban daban tare da basu tallafin gudanar da nasu sana’o’in, daga ciki akwai sana’ar dinki, gyaran gashi, kwamfuta, gini, walda, da dai sauransu.

“Bayan kammala samun horo, an raba ma dukkanin wadanda suka ci gajiyar wannan tallafi kayan aiki da zasu samar da nasu sana’ar tare da dogaro da kansu.” Inji Yau Babayi.

Bugu da kari, Yau, yace manufar gidauniyar shi ne inganta rayuwar gajiyayyu da marasa galihu dake cikin al’umma. Ya cigaba da cewa gidauniyar ta samar da ruwan burtsatsi ga wasu al’ummomi dake karamar hukumar Yola ta kudu, inda yace suna kokarin fadada aikin zuwa wasu yankunan.

Daga karshe, Yau Babayi yace a yanzu haka sun fara shirye shiryen samar da ababen kiwon lafiya da kuma kayan koya da koyarwa a makarantu domin amfanar da jama’an jahar gaba daya.

A wani labarin kuma, kaakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya dauki nauyin kulawa da wata jaririya mai suna Halima Abubakar da aka haifa da wata matsalar rashin lafiya a jahar Katsina, inda ya biya mata kudin asibiti a babban birnin tarayya Abuja.

Akwanakin baya ne Gbajabiamila ya hadu da wannan jaririya a sansanin yan gudun hijira yayin wata ziyara daya kai jahar Katsina, inda ya yi alkawarin daukan nauyin jaririyar, tare da bata kulawar daya kamata.

Mashawarcin Gbajabiamila a kan harkar yan gudun hijira, Hamza Baba, ya bayyana cewa iyayen jaririyar, Abubakar da Nafisa sun fito ne daga kauyen Wagini dake cikin karamar hukumar Batsari a dalilin ayyukan yan bindiga da suka addabi yankin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel