Jam’iyyar APC ta na neman kama Sanata Melaye kafin zabe – Inji PDP

Jam’iyyar APC ta na neman kama Sanata Melaye kafin zabe – Inji PDP

Mun ji cewa jam’iyyar hamayya ta PDP ta zargi Mia giram gwamnan jihar Kogi da kuma Darektan yakin neman zabensa watau Sanata Smart Adeyemi da yunkurin cafke Sanata Dino Melaye.

PDP ta ce gwamnan mai neman tazarce da kuma Smart Adeyemi su na kitsa hanyar da za su bi su cafke Dino Melaye, su garkame shi kafin zaben da za ayi Ranar 16 ga Watan Nuwamban nan.

Jam’iyyar ta ce Jagororin na APC sun kitsa wannan ne a wani taro da su ka yi a gidan gwamnatin jihar Kogi. Wani Hadimin Sanata Melaye mai suna Mista Gideon Ayodele, ya bayyana wannan.

A Ranar Talata, 5 ga Watan Nuwamban 2019, Gideon Ayodele ya fitar da jawabi ya na zargin gwammatin APC da kuma Sarkin yakin gwamnan Kogi da shirya yadda za a kama Maigidansa.

Jam’iyyar PDP ta na kira ga mutanen kirkin da ke yankin Yammacin Kogi da sauran jama’an Kogi, su tashi tsaye wajen ganin sun yaki da yunkurin yi masu fashin kuri’arsu a zaben da za ayi.”

KU KARANTA: Gwamna bai so ana kiransa 'Yallabai, ya ce a kira sa Gwamna kurum

Yahaya Bello ya na neman tazarce ne a jam’iyyar APC mai mulki yayin da Sarkin yakin neman zabensa, Smart Adeyami zai kara da Sanata mai-ci, Dino Melaye bayan kotu ta rusa zabensa.

Mai magana da yawun bakin Kwamitin yakin neman zaben APC a jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya karyata wannan zargi da aka jefawa APC inda ya ce kama mutane ba aikin gwamnan ba ne.

“Gwamna bai da sha’awar kama kowa, ko da Dino domin kuwa babu bukatar wannan. Ya riga ya fadi zabe domin kuwa ba ya kamfe tun da ya san babu abin da zai fadawa mutane, inji Fanwo.

A baya kun ji cewa wasu ‘yan takarar yankin Kogi ta Yamman sun janye takararsu inda su ka bi tafiyar Alhaji Yahaya Bello da Edward David Onoja, kuma su ka marawa Smart Adeyemi baya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel