Yanzu -Yanzu: Pantami dakatar da biyan tsabar kudi a ofisoshin NIPOST

Yanzu -Yanzu: Pantami dakatar da biyan tsabar kudi a ofisoshin NIPOST

Ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, Dr Ali Isah Ibrahim Pantami, ya bada umarnin daina biyan tsabar kudi a duk ofisoshin NIPOST dake fadin kasar na.

Ministan ya bada wannan umarnin ne sakamakon binciken da yayi cewa "marasa gaskiya na amfani da tsarin karbar tsabar kudin a hukumar NIPOST din don aiwatar da rashin gaskiya".

Dr. Pantami, a takardar da mai magana da yawunsa tasa hannu, Uwa Sulaiman, yace, hakan na daga cikin yaki da rashawan da shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa gaba kuma hakan yana daga cikin alhakin ma'aikatarsa. A don haka ne dokar zata fara aiki nan take. A dakatar da duk wani tsari ko shirin karbar tsabar kudi a duk ofisoshinsu na fadin kasar na.

"Na daga cikin alhakin shugaban kowanne ofishin NIPOST na kasar nan da ya samar da POS tare da takardar biyan kudi ta bankuna don cigaba da al'amuran ofisoshin a duka fadin kasar nan,"

DUBA WANNAN: Malami ya rage wa EFCC da ICPC iko, ya kankare wani babban kwamiti

"Ana sanar da jama'a da duk kwastomomin NIPOST da su koma mafani da POS don biya kudi da katin bankinsu a take ko kuma suyi amfani da takardar biyan kudi ta bankuna a duk lokacin da zasu yi kasuwanci da kowanne ofishin NIPOST,"

"Wannan umarnin na wucin gadi ne don datse hanyoyin rashawa da almundahanar kudade. Muna cigaba da aikin ganin yadda zamu gyara tsarin tare da shawo kan matsalar na dindindin."

A kuma cikin wannan halin ne, Dr Pantami yayi umarni ga shuwagabannin ofisoshin NIPOST da su kawo hanyoyin rage tsaiko akan cikawa kwastomomi aikyukansu. Ba za a lamunci bacin lokaci ba a karkashin ofishin mai girma ministan, wanda NIPOST take karkashin kulawarsa."

"Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ofishin mai girma ministan sadarwa da habaka tattalin arziki ta fasahar zamani na kokarin kare hakkin 'yan Najeriya kuma ba zasu lamunci rashawa ba komai kankantarta," Takardar da kare da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel