Yanzu-yanzu: Kwastam ta haramta sayar da fetur ga gidajen mai dake da kusancin 20km da iyakokin Najeriya

Yanzu-yanzu: Kwastam ta haramta sayar da fetur ga gidajen mai dake da kusancin 20km da iyakokin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bakin hukumar hana fasa kwabri wato Kwastam, ta bada umurnin daina sayarwa gidajen mai dake kimanin kilomita 20 da iyakokin Najeriya man fetur.

Kwantrola Janar da hukumar kwastam, Hameed Ali, ya bada umurnin ne a jawabin da wani mataimakinda Chidi, A ya fitar ranar 6 ga Nuwamba, 2019 kamar yadda Legit.ng ta gani.

Jawabin yace: " Kwantrola Janar na kwastam ya bada umurnin cewa daga yanzu kada a sake sayarwa gidajen mai da ke da kusancin kilomita 20 da iyakokinmu komin kankancinshi."

"Saboda haka a na kira ga ku dabbaka umurnin kai tsaye."

A wani labarin, Kwantrola Janar na hukumar hana fasa kwabrin, Kanar Hamid Ali, ya ce rufe iyakokin Najeriya da akayi zai yi matukar taimakawa cigaban kasar.

Yace: "Wannan gwamnati ce wacce ta lashi takobin cewa wajibi ne mu gina Najeriya, mu ci kayan noman Najeriya."

"Kasar Sin da muke zuwa siyo kusan dukkan kayayyakin da muke amfani da su, shin kun san shekaru nawa suka rufe iyakokinsu? Sun rufe iyakokinsu na tsawon shekaru 40 kuma gashi yau sun girma. Shin baku son Najeriya ta girma ne?"

Hakazalika Shugaba Hukumar DSS, Magaji Bichi, ya ce rufe iyakokin da Najeriya da gwamnatin tarayya tayi ya taimaka wajen rage fataucin makamai kuma ya taimakawa jami'an tsaro wajen lura da shiga da ficen mutanen da ka iya zama kalubale ga zaman lafiyar kasa.

Mista Bichi ya bayyana hakan ne a taron yaye daliban ilimin leken asiri da Abuja.

Ya roki gwamnati ta sanyawa iyakokin katangar karfe har sai lokacin da abubuwa suka daidaita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel