Wata uwa ta bayyana dalilinta na jefar da jinjirin da ta haifa a cikinta

Wata uwa ta bayyana dalilinta na jefar da jinjirin da ta haifa a cikinta

- Rundunar yan sandan jihar Ondo ta saki wata uwa mai shekara 23 wacce ta yasar da jinjirin da ta haifa dan watanni uku a titi sannan ta gudu

- Wasu bayin Allah ne suka tsinci jinjirin a yankin unguwar Ugbe Akoko da ke karramar hukumar Akoko North-East a jihar Ondo a makon da ya gabata, sannan suka kai rahoton lamarin zuwa ofishin yan sanda

- Monsuratu Arogundade uwar yaron wacce aka yi nasarar kamawa bayan afkuwar lamarin, ta ce ta rasa hankalinta ne lokacin da ta yanke shawarar jefar da jinjirin sannan ta roki gwamnati da ta dawo mata da danta

Hukumar yan sanda ta saki wata matashiyar mata, Monsuratu Arogundade, wacce ta yasar da jinjirinta dan watanni uku a titin unguwar Ugbe Akoko da ke karramar hukumar Akoko North-East a jihar Ondo a makon da ya gabata.

Arogundade mai shekara 23 ta jefar da jinjirin nata a kan titi sannan ta gudu, amma wasu bayin Allah suka tsinci dan sannan suka kai rahoton lamarin ga yan sanda.

An tattaro cewa daga bisani an mika jinjirin ga jami'an ma'aikatar kula da harkokin mata da cigaban jama'a.

Arogundade ta bayyana a ofishin wani lauya a Ikare Akoko, Mista Lanre Kareem, cewa ta rasa hankalinta ne lokacin da ta yanke shawarar jefar da jinjirin sannan ta roki gwamnati da ta dawo mata da danta.

"Ina so na roki gwamnati da ta yi mani afuwa sannan ta mayar mani da dana; ban san mai nake yi ba a wannan rana; na rasa hankalina a wannan lokacin," cewarta.

KU KARANTA KUMA: APC da PDP sun yi martani bayan kotun daukaka kara ta sallami kakakin majalisar dattawa sannan ta ba Olujimi kujerarsa

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Mista Femi Joseph, ya ce ba a hukunta uwar bane saboda jaririn.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel