Majalisar Wakilan Tarayya za ta binciki Hukumomin PPRA da PPPRA

Majalisar Wakilan Tarayya za ta binciki Hukumomin PPRA da PPPRA

Mun samu labari cewa majalisar wakilai za ta yi bincike a kan hukumomin PPMC da PPPRA masu kula da kasuwancin kayan mai da kuma masu lura da kula farashin kayan mai a Najeriya.

‘Yan majalisar za su binciki hukumomin ne a dalilin sauyin da ake samu na mai a gidaje. Majalisar ta lura cewa ana samun banbanci a kan farashin da ‘yan kasuwa su ke su ke saida fetur.

Daily Trust ta rahoto cewa majalisar ta cin ma wannan matsaya ne bayan wata takarda da wasu ‘yan majalisun jam’iyyar APC su ka gabatar ya gabatar a Ranar Laraba, 6 ga Watan Nuwamba.

Honarabul Odebunmi Olusegun Dokun na jihar Oyo da kuma Takwaransa, Abubakar Hassan Fulata na jihar Jigawa ne su ka tado wannan magana wanda sauran ‘yan majalisar su ka amince.

KU KARANTA: Majalisa na kokarin kawo kudirin da zai kai Malaman Jami’a gidan yari

Sunan da aka yi takardar lakabi shi ne: “Need to Check the Discriminatory Practices of the Petroleum Products Marketing Company Limited and the Petroleum Products Pricing Regulatory Agency against the Independent Petroleum Marketers on the Sale of Premium Motor Spirit.”

Wannan batu zai duba banbance-banbancen da ake samu wajen saida fetur a sakamakon aikin hukumar PPMC mai kula da kasuwancin kayan mai da PPPRA mai lura da farashin mai a kasar.

‘Yan majalisan sun ce hukumomin na kamfanin mai, NNPC, da su ke da alhakin raba mai ga manya da kananan ‘yan kasuwa ba su rasa hannu wajen banbancin da ake samu na farashin mai.

Hon. Olusegun Dokun da Hon. Abubakar Fulata sun fadawa zauren majalisar cewa akwai bukatar ayi bincike na musamman domin duba abin da ya sa ake samun sauyi wajen farashin litar fetur.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel