APC da PDP sun yi martani bayan kotun daukaka kara ta sallami kakakin majalisar dattawa sannan ta ba Olujimi kujerarsa

APC da PDP sun yi martani bayan kotun daukaka kara ta sallami kakakin majalisar dattawa sannan ta ba Olujimi kujerarsa

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da People’s Democratic Party (PDP) a jihar Ekiti sun yi martani ga hukucin kotun daukaka, wacce ta soke nasarar Dayo Adeyeye na APC, inda ta kaddamar da Sanata Biodun Olujimi ta PDP a matsayin wacce ta yi nasara.

Kotun daukaka karar a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba ta riki hukuncin kotun zabe na ranar 10 ga watan Satumba karkashin jagorancin Justis Danladi, wanda ya umurci INEC da ta janye takardar shaidar cin zaben da ta baiwa Adeyeye sannan ta mika sabo ga Olujimi.

Da suke martani kan hukuncin, jam’iyyar APC mai mulki da PDP sun bayyana ra’ayinsu mabanbanta kan hukuncin.

Yayinda jam’iyyar adawa ke yaba ma hukuncin kotun na tabbatar da nasarar yar takarar jam’iyyar, ta bayyana hakan a matsayin gaskiya ta yi halinta.

Jam’iyyar ta bayyana cewa hukuncin kotunan zaben da na daukaka kara bai zo masu a bazata ba saboda sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana bai yi daidai da ainahin zaben da aka kada ba.

Amman APC tace sallamar kakakin majalisar dattawan ya sabama muradin mutane.

A wani jawabi daga sakataren labaran PDP a jihar, Mista Jackson Adebayo, jam’iyyar ta soki INEC akan hada kai da jam’iyyar APC wajen sace kuri’un da aka ba Sanata Olujimi da PDP a zaben ba tare da kula da makomar damokradiyya a kasar ba.

Jam’iyyar ta kuma jinjina ma bangaren shari’a akan gyara kuskuren da aka yi ta hanyar kaddamar da Sanata Olujimi da PDP a matsayin ainahin wacce ta lashe zaben majalisar dokokin tarayya.

Jam’iyyar ta bukaci dukkanin shugabanni da mambobin jam’iyyar da su kalli nasarar a matsayin nufin Allah, don haka akwai bukatar hadin kai domin inganta jam’iyyar zuwa gaba.

Daraktan labaran APC, Elder Sam Oluwalana, ya bukaci mutane da kada su bari gwiwarsu ya karye akan hukuncin kotun, cewa su cigaba da marawa APC a jihar baya domin gyara barnar da gwamnatin da ta shige ta yi wa tattalin arzikin jihar.

KU KARANTA KUMA: Kudirin kara VAT ya tsallake mataki na biyu a zauren Majalisar Dattawa

Oluwalana ya bayyana cewa dan gajeren lokacin da sanata Adeyeye ya yi a majalisar dattawan ya yiwa mutanen Ekiti ta Kudu da jihar bakin daya gagarumin kokari.

Ya kuma roki mutane da su cigaba da gudanar da harkokin gabansu maimakon daukar doka a hannunsu kan hukuncin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel