Babbar magana: Yadda mata suka yi zanga-zanga tsirara kan rushe wasu gine-gine

Babbar magana: Yadda mata suka yi zanga-zanga tsirara kan rushe wasu gine-gine

'Yan kasuwa mata a Igbokoda, hedkwatar karamar hukumar Illaje da ke jihar Ondo a jiya sunyi zanga-zanga akan yunkurin gwamnatin jihar na rushe wasu gine-gine da aka yi a babbar kasuwar Igbokoda.

Zanga-zangar da ta dauki tsawon sa'o'i hudu, ta jawo cushewar manyan titunan garin sakamakon shinge da masu zanga-zangar suka saka a titunan shiga kasuwar kamar yadda jaridar The Nation Onilne ta ruwaito.

Jami'an gwamnatin jihar sun yi yunkurin rushe gine-ginen da gwamnatin ta kwatanta da cewa sunyi su ba bisa ka'ida ba. Amma kuma, sai matan suka soki abinda gwamnatin tayi kudirin yi.

Sunyi ikirarin cewa gwamnatin bata sanar dasu ta yadda ya dace ba. Masu zanga-zangar sun koka akan halayya jami'an gwamnatin.

DUBA WANNAN: Titunan Najeriya basa cikin mummunan hali, in ji ministan Buhari

Babban sakataren cibiyar kasuwancin gwamnatin jihar ondo, Mr Sunday Lebi, yace gwamnatin ba zata lamunci rashin biyayya ba. Ya ce, gwamnati ta fusata da abinda matan suka yi da ya hana jami'an aiwatar da abinda ya kaisu kasuwar.

Lebi yace, jami'an gwamnatin sun kasa aiwatar da nufinsu saboda tsirara da matan suka yi yayin zanga-zangar kuma sun yi amfani da miyagun kalamai akan jami'an.

Yace, cibiyar na da damar maida kasuwar yadda ya dace don samun damar karuwar kudin shiga ga lalitar gwamnatin jihar.

Lebi yace, karantsaye ne ga dokar jihar karin gini wanda zai zamo ya kare hanyar tafiyar mutane da ababen hawa.

Yace: "Mun je don yin abinda ya kamata bayan mun tattauna dasu shekaranjiya tare da sanar dasu anyi hakan ga sauran kasuwannin jihar. Gini ba bisa tsari da ka'ida ba yana lalata kasuwa kuma hatsari ne ga rayuka da ababen hawa dake shige da fice a kasuwar."

Babban sakataren yace, gwamnatin jihar zata cigaba da amfani da hanyoyin da ya dace don tabbatar da kasuwannin gwamnatin jihar sun kasance cikin halin da yakamata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel