Majalisa ta na tanadin hukuncin dauri ko tara ga masu saba doka a kafafen sadarwa

Majalisa ta na tanadin hukuncin dauri ko tara ga masu saba doka a kafafen sadarwa

Majalisar dattawan Najeriya ta sake dawo da kudirin da zai tsabace kafafen sadarwan zamani. Wannan kudiri zai taimaka wajen yakar karya a shafukan yanar gizo da zumunta a Najeriya.

Daily Trust ta rahoto cewa an saurari wannan kudiri a karon farko a majalisar dattawan a Ranar 6 ga Watan Nuwamba, 2019. Kudirin ya na cikin kudirori goma sha daya da aka zauna a kansu jiya.

Sunan da aka sa wa kudirin shi ne ‘The Protection from Internet Falsehood and Manipulations Bill 2019’ Ma’ana kudirin bada kariya daga sharri wajen amfani da shafukan yanar gizo na 2019.

Wanda ya gabatar da wannan kudiri a gaban majalisar kasar ya ce zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiyar Najeriya. Sanatan ya bayyanawa ‘Yan jarida haka ne a Ranar Laraba a Garin Abuja.

“Ba hana mutane amfani da shafukan yanar gizo su wallafa abin da su ke ganin ya dace za a yi ba, amma mu na ganin ba daidai ba ne amfani da wannan kafa ka yada bayanin da ba gaskiya ba.”

KU KARANTA: Majalisar Dattawa ta fara amincewa da shirin kara VAT

‘Dan majalisar ya ce kudirin zai yi maganin masu hawa kan shafukan sadarwan zamani su wallafa abin da sun san ba gaskiya ba ne amma su yi hakan saboda kokarin cin ma wani burinsu.

Rahotannin sun ce kudirin ya yi tanadin hukuncin daurin shekaru uku ko kuma tarar kudi N150, 000 ga duk wanda aka samu da laifi. Idan kudirin ya zama doka, zai yi aiki har a kan kamfanoni.

Duk kamfanin da ya ki dakile wani bayani da aka wallafa na karya bayan hukuma ta sanar da shi kan hadarin yadawa jama’a, zai biya tarar Naira miliyan biyar zuwa miliyan goma inji Sanatan.

Dazu kun ji labari duk Malamin makarantar da aka samu ya na taba, ko runguma, ko damke mama ko kutiri ko wani sashe na jikin ‘Daliba kamar kwankwasonta zai iya tafiya kurkuku.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel