Kudirin kara VAT ya tsallake mataki na biyu a zauren Majalisar Dattawa

Kudirin kara VAT ya tsallake mataki na biyu a zauren Majalisar Dattawa

Wani kudirin haraji da ke gaban majalisa da nufin kara VAT na wasu kayan masarufi ya samu shiga a majalisa. Yanzu haka yunkurin dada VAT daga 5% zuwa 7.5% ya haura mataki na biyu.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust jiya, wannan kudiri ya tsallake matakin farko da na biyu duk da korafin da wasu Sanatoci su ka nemi su yi na cewa ba su san komai kan batun ba.

A Ranar Laraba, 6 ga Watan Nuwamba, majalisar dattawan kasar ta sake sauraron kudirin inda yanzu ake jira a kai zuwa sauraro na uku wanda shi na karshe, kafin a karkare a mikawa shugaban kasa.

Wasu Sanatocin sun koka da cewa ba a ba su takardar abin da wannan kudiri ya kunsa ba. Amma shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, bai saurari wannan ba, inda ya yi fatali da zancensu.

KU KARANTA: Abin da jama'a ke fada game da shirin kara harajin VAT

Shugaban masu rinjaye a majalisa, Sanata Yahaya Abdullahi ya yi jawabi inda ya bayyana fa’idojin wannan kudiri wanda su ka hada samawa gwamnati kudin shiga da gina abubuwan more rayuwa.

Sanatan na Arewacin Kebbi ya bayyana cewa wannan mataki da ake so a dauka na dada haraji zai taimaka wajen kara saukaka kasuwanci a Najeriya tare kawo gyara a harkar harajin kasar baki daya.

Sanatar Adamawa ta Kudu, Binos Yaroe, ce ta fara kokawa a game da kudirin inda ta ce ya kamata ace majalisa ta rabawa kowa takardu domin su fahimci abin da ya kunsa kafin a iya cigaba da muhawarar.

Ita ma Sanata Betty Apiafi ta Ribas, ta gabatar da irin wannan korafi ta na mai cewa duk da maganar ta yi nisa, ba ta san abin da kudirin ya kunsa ba. Ahmad Lawan ya ce dama hakan bai zama dole ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel