NEITI: Dala biliyan 38.5 da danyen mai sun fada hannun Barayi a cikin shekaru 10

NEITI: Dala biliyan 38.5 da danyen mai sun fada hannun Barayi a cikin shekaru 10

Danyen mai da tacaccen man fetur da aka sace a Najeriya a cikin shekaru goma da su ka wuce sun kai na Dala biliyan 41.9 kamar yadda hukumar nan ta NEITI ta fitar a wani sabon rahoton ta.

Hukumar NEITI ta wallafa binciken da ta yi ne a Ranar Laraba 6 ga Watan Nuwamba, 2019 a babban birnin tarayya Abuja. Binciken ya na nuna cewa an saci danyen mai na Dala biliyan 38.5.

Haka zalika an yi wa Najeriya satar abin da ya kai Dala biliyan 1.6 na man gida da kuma wasu Dala biliyan 1.8 a kan tacaccen fetur da sauransu. An tafka wannan ne tsakanin 2009 da 2019.

Jaridar nan ta Daily Trust ta kasar nan ce ta rahoto labarin wannan bincike da NEITI ta yi. An sa wa takardar binciken suna “Bankado badakalar satar danyen man da ake yi wa Najeriya.”

KU KARANTA: Majalisa ta na so Hukumar FERMA ta nganta wasu ribabbun hanyoyi

Hukumar ta bada shawara ga gwamnatin tarayya ta yi amfani da dabarun kimiyya na tantance zanen yatsu wajen jigilar mai domin kawo karshen wannan muguwar annobar da ta addabi kasar.

Bayan nan kuma NEITI ta bukaci a yi wa kayan sufurin man lamba tare da kawo wasu dabaru da za su hana satar arzikin Najeriya. Shekara da shekaru kenan an gaza magance wannan matsala.

A yayin da Najeriya ta ke fama da matsalar karancin kudin shiga, NEITI ta nemi gwamnati ta karkato da hankalinta kan kasurgumar satar da ake tafkawa a bangaren arzikin mai da kuma gas.

Abin da ake asara a duk rana ya kai Dala miliyan 11. A wata kuma, ana rasa Dala miliyan 349 da kuma biliyan 4.2 a shekara. Magance matsalar satar mai zai inganta kudin shigan kasar.

Wadannan kudi su na shiga hannun masu sabawa doka da masu fasa butun mai ne. Ganguna 200, 000 zuwa 400, 000 ake sacewa kullum, ma’ana daya cikin biyar na man Najeriya ake sacewa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel