Malami ya rage wa EFCC da ICPC iko, ya kankare wani babban kwamiti

Malami ya rage wa EFCC da ICPC iko, ya kankare wani babban kwamiti

Ministan shari'a, Abubakar Malami (SAN) ya rage karfin ikon hukumar yaki da rashawa ta EFCC da sauran hukumomin yaki da almundahanar kudade na Najeriya.

Ministan ya sauke duk kwamitin karbo kadarori da kudaden da aka wawura na Najeriya.

Ministan ya bada umarni ga hukumomin cewa, duk wata shari'a da ta danganci karbo kudi ko kadarar da aka sata a Najeriya kafin a yanke hukunci sai ta fara biyowa ta ofishinsa.

Hakazalika, duk wasu kudaden ko kadarorin da aka samo zasu dinga shiga ta ofishinsa ne.

Takardar da ta bada umarnin na tun a ranar 29 ga watan Oktoba tace, "Duk wata shari'ar da ba a kammala ba da ta danganci kwace kudi ko kadarar da aka sata, za a maido da ita ofishin ma'aikatar shari'a ne,"

DUBA WANNAN: Abba Kyari ya fi Osinbajo karfin iko: 'Yan Najeriya sun mayarwa dan majalisar APC martani

A baya, hukumar yaki d arshawa ta EFCC tana da ikon fara kwace kadara a shari'ar da ba a kammala ba kamar yadda ya faru da matar tsohon shugaban kasar Najeriya, Patience Jonathan.

Sabon umarnin kuwa na bayyana cewa, duk ire-iren matsalolin nan shugaban ma'aikatar shari'ar ne kadai zai iya magancesu.

Takardar ta kara da bayyana cewa, duk wata kadara ko kudi da aka kwace, toh tilas ne duk ma'aikatu, bangarori da cibiyoyin da suka shafa suyi musu rijista.

Ta kara da cewa, duk wasu kadarori ko kudi da ka kwace, toh za a mika su ga shugaban ma'aikatar shari'ar a cikin kwanaki 60 ne daga ranar da aka karbesu. Ya kara da cewa, duk wani lamari da ya danganci fada da rashawa ko almundahanar kudade, za a yi shi ne da yardar ministan.

Ministan ya ja kunne akan cewa, duk wata cibiya da ta kuskure tayi karantsaye ga dokoin nan, zata fuskanci hukuncin da ya dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel