Yanzu - Yanzu: Maina ya bayyana a kotu kan keke guragu

Yanzu - Yanzu: Maina ya bayyana a kotu kan keke guragu

Tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, AbdulRasheed Abdullahi Maina ya bayyana a yau gaban kotu a keken guragu kamar yadda gidan talabijin na TVC suka wallafa.

Tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, AbdulRasheed Maina, a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba ya bayyana gaban babban kotun tarayya dake Abuja a keken guragu.

Maina, wanda yake sanye da kaftani mai launin sararin samaniya ya iso gaban kotun ne don ta yanke hukunci akan bukatar belin da ya mika gabanta ta hannun lauyansa.

Yayin da mai shari'ar ya bayyana a gaban kotun, jami'an tsaro da na gidan yarin sun hana manema labarai daukar hoto ko bidiyon wanda ke kare kansan.

DUBA WANNAN: Daga Amalala: Yayarta tayi mata mugun dukan da yayi ajalinta

Jami'an sun kara da barazanar fatattakar duk wani dan jarida da yayi yunkurin daukar hoto a cikin kotun.

Legit.ng ta gano cewa, tuni tsohon shugaban hukumar fanshon ya bayyanawa kotun cewa rashin lafiya ta kada shi yayin da yake tsare a gidan yari bayan umarnin da kotun ta bada.

Har yanzu dai ba a kira shari'ar ba saboda kotun na sauraron wasu al'amura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel