Kotu ta hana dauke 'dan maina daga ofishin yan sanda zuwa kurkuku

Kotu ta hana dauke 'dan maina daga ofishin yan sanda zuwa kurkuku

Babbar kotun tarayya dake Abuja ta yi watsi da bukatar Faisal, 'dan tsohon shugaban kwamitin gyarar kudin fanshi, AbdulRashid Maina, na daukeshi daga ofishin yan sanda zuwa gidan yari tare da mahaifinsa.

An fara gurfanar da Faisal a ranar 25 ga Oktoba, 2018 kan laifin almundahana da amfani da asusun banki da ya sabawa doka

Lauyoyin EFCC sun yi zargin cewa tsakanin 2013 da 2019, Faisal ya karbi N58.11million na kudin da mahaifinsa ya sata daga asusun al'umma.

Lauyansa, Francis Oronsaye, ya bukaci kotun ta mayar da Faisal kurkukun Kuje dake Abuja, inda mahaifinsa ke zaune a yanzu.

Oronsaye ya bayyana cewa sun bukaci hakan ne saboda ana hanashi ganin Faisal a ofishin yan sanda.

Yayin yanke hukunci, Alkali Okong Abang ya yi watsi da bukatar, ya ce ba za'a mayar da shi ba.

Ya dage karar zuwa ranar 21 da 22 ga Nuwamba domin cigaba da zaman kotu.

KARANTA: Akwai kura, Jonathan, Wike da wasu manyan PDP sun kauracewa taron kamfe a Bayelsa

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta bayyana cewa mahaifin Faisal, AbdulRashind Maina ba mutumin kirki bane kuma bai ganin girman dokar Najeriya.

Hukumar ta ce idan har aka bashi beli, tabbas guduwa zai yi daga Najeriya.

Hukumar ta ce Maina ya yi rub da ciki da Bilyan 3 na yan fansho a fili ba tare da wani boye-boye ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel