Akwai kura, Jonathan, Wike da wasu manyan PDP sun kauracewa taron kamfe a Bayelsa

Akwai kura, Jonathan, Wike da wasu manyan PDP sun kauracewa taron kamfe a Bayelsa

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, gwamnan jihar RIbas, Nyesom Wike da Timi Alaibe wanda ya zo na biyu a zaben fida gwanin PDP a Bayeksa, sun kauracewa yakin neman zaben da jam'iyyar ta gudanar na musamman.

Taron kamfen da aka gudanar ranar Laraba a Oxbow Lake Pavalion a Bayelsa ne taron kaddamar da yakin neman zaben gwamnan da zai gudana 16 ga Nuwamba, 2019.

Shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, ya gargadi jami'an tsaro kan amfani da su wajen magudin zabe.

A bangare guda, matasan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun yi zargin cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na diban makiyaya domin haddasa rigima da kuma magudin zabe ta yadda su za su yi nasara.

Da suke nuna damuwa kan lamarin, matasan na PDP karkashin inuwar ‘PDP South-south Youth Vanguard’ sun zargi APC da rashin goyon bayan gwagwarmayar Ijaw, amma sun shawarci jam’iyyar da ta janye daga duk wani launi na rikici a lokacin zabe.

Matasan, a wani jawabi daga shugabansu na kasa, James Efe Akpofure, sun yi zargin cewa abunda APC ke muradi kawai shine man fetur a dake jihar Bayelsa, cewa jam’iyyar bata da ra’ayi a cigaban jihar.

Matasan na PDP sun bayyana cewa a koda yaushe APC na neman hanyar mallakar akalla jiha guda daga yankin mai albarkatun man fetur, inda suka yi zargin cewa wannan ne dalilin da yasa jam’iyyar ta tayar da fitina a lokacin zaben gwamnan jihar Rivers.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel