Dan wasan kwallon kafa ya shiga tsaka mai wuya a kan laifin kisan kaza

Dan wasan kwallon kafa ya shiga tsaka mai wuya a kan laifin kisan kaza

A ranar Laraba ne wata kungiyar rajin kare hakkin dabbobi tace zata maka wasu 'yan kwallon kasar a kotu sakamakon haurin wata kaza da sukayi har ta rasa ranta a yayin wani wasan gogewa da sukayi a karshen mako.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi yayin da wasu gungun kaji suka afka filin wasan kwallon kafa da ke gabashin Croatia.

Daya daga cikin 'yan wasan, Ivan Gazdek daga kungiyar NK Jelengrad, ya afkawa tsunysayen ne inda ya hauri daya daga ciki har ta tsallake katanga inda daga baya ta mutu.

DUBA WANNAN: Ire-iren abinci 5 da ya kamata dan adam ya guda kafin kwanciya barci

An dakatar da matashin mai shekaru 23 daga wasan saboda bai nuna ladabi ga wasanni ba.

Kungiyar sa kan ta kushe lamarin tare da cewa "wannan abun kunya ne kuma rashin gwarzanta ne da har dan wasan kwallon kafa zai kashe dabba".

Kungiyar tace zata maka shi gaban kuliya akan laifin 'azabtar da dabbar har da kisa'.

In kuwa aka gurfanar dashi kuma aka kama shi da laifi, to ba shakka zai yi shekara daya a gidan gyaran hali.

Gazdek, wanda yayi ikirarin shima masoyin dabbobi ne saboda mallakarsu da yayi, yace bai yi da ganganci ba balle niyya.

"Naso korar dabbobin ne amma kafata ta shure daya bisa tsautsayi," in ji shi.

"Kaji suna yawan zuwa filin wasan kuma suna tsayar mana da wasanmu. Filin wasan ciki yake da kazantarsu, wannan kuwa rashin tsafta yake kawowa," ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel