Gwamnatin Buhari za ta kashe naira biliyan 58.48 a ginin babbar hanyar Neja zuwa Kwara

Gwamnatin Buhari za ta kashe naira biliyan 58.48 a ginin babbar hanyar Neja zuwa Kwara

Majalisar zartarwa ta gwamnatin Najeriya ta amince da kashe zunzurutun kudi naira biliyan 58.48 domin sabunta babbar hanyar data hada jahar Neja da jahar Kwara daga Bida-Saachi-Nupeko da kuma gadar Nupeko-Pategi.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola ne ya sanar da haka yayin da yake ganawa da manema labaru bayan kammala taron majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa dake Aso Rock Villa, inda yace tsohon kwangila ne, amma aka dakatar da shi domin sake yin nazari a kansa.

KU KARANTA: Majalisar dokokin jaha ta amince da nadin kwamishinoni 23 a gwamnatin Adamawa

A cewar Fashola: “Kun ji cewa aikin hanyar ya fara ne daga Bida-Saachi-Nupeko, a yanzu mun kara har da gadar data hada Nupeko da Pategi ta cikin tafkin Neja domin ta hade jahohi Kwara da Neja tare da hada yankin kudu maso yammaci da Arewa maso tsakiya.

“Tsohon kwangila ne, tun a shekarar 2013 aka bayar da shi, amma aka dakatar dashi saboda rashin yin ingantaccen aiki, muka sake nazari a kansa, a baya babu gada a cikin aikin, amma a yanzu mun sanya gada a ciki, a yanzu kudin aikin ya kai N58.488bn, kuma a watanni 30 za’a kammala shi.” Inji shi.

Fashola ya shaida ma kamfanin dillancin labaru cewa ruwan sama ya kawo tsaiko ga ayyukan ginawa da gayaran hanyoyi, amma yana fatan da zarar ruwa ya dauke ayyukan zasu cigaba.

Daga karshe ya tabbatar ma matafiya dake bin titunan Najeriya cewa suna aiki tukuru domin gudanar da ayyukan hanyoyi, tare da tabbatar da basu tare ma matafiya hanyoyin tafiya ba saboda zuwan bukukuwan karshen shekara.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi wasu sabbin nade naden hadimai masu muhimmanci a gwamnatinsa da zasu taya shi gudanar da ayyukansa da manufofinsa wajen cika ma jama’an jahar Kaduna alkawurran daya daukan musu.

Kaakakin gwamnan jahar Kaduna, Muyiwa Adekeye ne ya sanar da wadannan sabbin nade inda yace gwamnan Kaduna ya amince da nadin tsohon babban ma’aikacin jaridar Daily Trust, Malam Ibraheem Shehu a matsayin mataimaki na musamman a harkar kafafen watsa labaru da hulda da jama’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel