Yanzu-yanzu: Kotu ta bayar da umurnin sakin Sowore

Yanzu-yanzu: Kotu ta bayar da umurnin sakin Sowore

Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umurnin sakin, Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar ADC a zaben Fabrairun 2019 kuma jagoran 'yan neman juyin juya hali wato #RevolutionNow kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A baya, lauyansa, Femi Falana (SAN) ya ce an cika dukkan ka'idojin bayar da belinsa da kotu ta gindaya.

Femi Falana ne ya bayyana haka a yau Laraba, 6 ga watan Nuwamba, inda yace Omoyele Sowore tare da abokina Olawale Bakare sun cika sharuddan beli a kan tuhume tuhumen cin amanar kasa da gwamnatin Najeriya ke musu kamar yadda Punch ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Ire-iren abinci 5 da ya kamata dan adam ya guda kafin kwanciya barci

Idab ba a manta ba, a kwanakin baya ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a garin Abuja ta sassauta sharuddan belin da ta gindaya ma shugaban kawo juyin juya hali a Najeriya, kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters.

Alkalin kotun, Ijeoma Ojukwu ce ta yanke wannan hukunci a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba inda tace ta rage masa kudin beli naira miliyan 100 da ta sanya masa zuwa naira miliyan 50, sa’annan ta rage sharadin beli na naira miliyan 50 ga Bakare zuwa naira miliyan 20.

Kazalika Alkali Ojukwu ta sassauta sharadin cewa lallai sai masu tsaya ma mutanen biyu sun ajiye shaidan suna da kwatankwacin wannan kudi a asusunsu da kotu, inda tace ta janye wannan sharadin shima.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel