Abba Kyari ya fi Osinbajo karfin iko: 'Yan Najeriya sun mayarwa dan majalisar APC martani

Abba Kyari ya fi Osinbajo karfin iko: 'Yan Najeriya sun mayarwa dan majalisar APC martani

- Dan majalisar wakilai na jam'iyyar APC, Akin Alabi ya ce Abba Kyari yafi Osinbajo karfin iko a mulkin tsarin mulkin Najeriya

- Hakan kuwa ya biyo bayan tashi da shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin ya yi takanas ta Kano har Landan don kai wa shugaban kasar takardu don ya rattaba hannu

- Wannan rubutun dan majalisar ya wallafa a shafinsa na Twitter ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta

'Yan Najeriya sun mayar da martani ga dan majalisa mai wakiltar Egbeda da Ona Ara ta jihar Oyo a tarayya, Akin Alabi akan ikirarin da yayi na cewa, Abba Kyari, shugaban ma'aikatan gidan gwamnati yafi mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo iko a Najeriya.

Alabi dan jam'iyyar APC ne kuma ya yi ikirarin ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata.

Idan zamu tuna, a ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu a kan gyaran dokar hakar man fetur da ke kasan ruwa a birnin Landan. Ya sa hannun ne a gaban shugaban ma'aikatan fadarsa, Abba Kyari.

DUBA WANNAN: Ire-iren abinci 5 da ya kamata dan adam ya guda kafin kwanciya barci

Wannan abu kuwa shi ya ja ikirarin Alabi a shafinsa na Twitter.

Lafuzzan Alabi sun jawo cece-kuce a kafofin sada zumunta. Ga kadan daga cikin tsokacin mutane.

"Ko kana so, ko baka so, shugaban ma'aikata yafi yafi kusanci da shugaban kasa akan mataimakin shugaban kasa. Wannan ba abun mamaki bane," In ji wani mai tsokaci.

"Mr Akin... Akwai bukatar a adana wannan rubutu naka. Don zai yi amfani ko nan gaba. Babu matsala...." in ji wani.

"Alabi na da gaskiya. 'Iko' ba yana nufin zai iya zartar da hukunci da kanshi bane. Yana nufin shugaban ma'aikatan na da kusanci sosai da shugaban kasar. Yana da ta cewa akan tsaro, mulki da rayuwar shugaban kasar. A wata siga kuwa, yafi mataimakin shugaban kasar iko," inji wani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel