Mukaddashin Shugaba: Manyan matakan da Osinbajo ya taba dauka

Mukaddashin Shugaba: Manyan matakan da Osinbajo ya taba dauka

Yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tare a kasar Ingila inda ya ke sararawa har zuwa Ranar 17 ga Watan Nuwamba, ya bar Najeriya ba tare da ya mikawa mataimakinsa mulki ba.

Daga Birtaniya dai shugaban kasar ya sa a hannu a kan wani kudiri da majalisa su ka amince da shi. Ganin haka ya sa aka dawo da korafin cewa Abba Kyari ya na da ikon da ya zarce kima.

Wannan mataki da shugaban kasar ya dauka ya dade ya na jawo surutu da ce-ce-ku-ce. Yanzu dai Daily Trust ta kawo jerin wasu ayyukan da Yemi Osinbajo ya yi a lokacin da ya samu dama.

1. EFCC: Ibrahim Magu

Bayan wata tafiyar shugaban kasar ne Mataimakinsa ya aika takarda ga majalisa domin ta tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC. A karshe Sanatoci ba su yi hakan ba.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari da Osinbajo su na nan yadda aka san su

2. CJN: Walter Samuel Onnoghen

A farkon 2017 ne Farfesa Yemi Osinbajo ya aika sunan Walter Samuel Onnoghen gaban majalisa domin a tabbatar da shi a matsayin Alkalin Alkalai. Bayan tabbatar da shi, daga baya ya bar kujerarsa.

3. Tsige Lawal Daura daga DSS

Wani babban matakin da Yemi Osinbajo ya dauka a lokacin da ya ke rike da Najeriya shi ne sauke Mista Lawal Daura daga kujerar shugaban hukumar DSS bayan jami’ansa sun zagaye majalisar tarayya.

4. SARS zuwa FSARS

Haka zalika yayin da ya ke kan kujerar mukaddashin shugaban kasa, Osinbajo ya rusa hukumar SARS inda ya maida ta FSARS bayan koke-koken dinbin jama’a game da zaluncin jami’an tsaron a Najeriya.

Ana rade-radin cewa wasu matakan da Osinbajo ya dauka sun hada shi fada da na-kusa da Mai gidansa. Dama can ana zargin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasan da rike madafan iko.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel