‘Yan Majalisa su na so Gwamnati da FERMA ta taba titunan Jihar Osun

‘Yan Majalisa su na so Gwamnati da FERMA ta taba titunan Jihar Osun

- ‘Yan Majalisar Tarayya sun yi kira a gyara manyan titunan da ke Jihar Osun

- An nemi Kwamitocin Majalisar su hada kai da Gwamnati da kuma FERMA

- ‘Yan Majalisar Wakilan sun kuma nemi a gina gadar da ke cikin Garin llie

A Ranar Laraba, 5 ga Watan Nuwamba, 2019, majalisar wakilan tarayya ta tsaida matsaya cewa kwamitocin ma’aikatar ayyuka da hukumar FERMA su dage wajen ganin an gyara titunan Osun.

Kamar yadda mu ka samu labari, an umarci wadannan kwamitocin su zauna da ma’aikatar gwamnatin tarayya da hukumar FERMA mai kula da hanyoyi domin a duba lamarin titunan jihar.

Majalisar ta bukaci a gyara titin Ende zuwa Ore wanda ya ratsa har zuwa cikin Ore-Ilie-da kuma ta Ilosin/Ogbomoso. An kuma nemi gwamnati ta sake tada gadar da ta hada mutanen Yankin Ilie.

KU KARANTA: Kamfanin Dangote zai maida hankali kan noman shinkafa

‘Dan majalisar jihar Osun a majalisar tarayya, Afolabi Rasheed Olalekan, shi ne ya tado maganar. Honarabul Rasheed Olalekan ya ke cewa hanyoyin su na matukar bukatar gyara a halin yanzu.

Olalekan wanda ke wakiltar Mazabar Odo-Otin, da Boripe/Ifelodun a majalisar tarayya ya ce tun 2011 aka bada kwangilar gadar Ilie zuwa rafin Erinle. Ya ce ya kamata ace an gama aikin a 2012.

‘Dan majalisar ya ce rashin gadar nan na iya kara jawo zaizayewar kasar wannan yanki saboda rashin wurin wucewan ruwa wanda a karshe ya ke afkawa cikin gidaje da gonakin mutanen Gari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel