Gwamnan APC ya bukaci a cire lakabin 'Your Excellency' daga sunansa

Gwamnan APC ya bukaci a cire lakabin 'Your Excellency' daga sunansa

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da cewa yana shirin cire 'Your Excellency' ma'ana mai 'Mai girma' daga sunansa kamar yadda ya ke a al'addan sunayen gwamnoni kamar yadda The Cable ta ruwaito a ranar Laraba 6 ga watan Nuwamba.

Sanwo-Olu ya ce, ubangiji kadai ne yakamata a kira da 'Mai girma'. Babu wani mutum da yake da nagartar wannan sunan.

Ya ce ya na son kawo karshen girman kai da lakabin ke janyo wa ne hakan yasa dole ya cire lakabin daga sunansa.

Ya ce, "A cikin watanni biyar da na yi aiki a matsayin gwamnan jihar Legas, na fahimci wasu abubuwa da suke bukatan garambawul game da alakar da ke tsakanin al'umma da gwamnati don inganta rayuwar al'ummar mu.

DUBA WANNAN: Ire-iren abinci 5 da ya kamata dan adam ya guda kafin kwanciya barci

"Hakan kuwa ya nakasa wadanda aka zaben, masu aikin don mutane, wadanda kuma mutane ke biya da harajinsu. Ana ganinsu a matsayin wadanda basa laifi kuma dole a bauta musu, a maimakon su dinga bautawa mutanen da suka zabesu. Ko ma dai menene tushen wannan camfi, dole ne mu zamo masu gaskiya. Ofisoshinmu cike suke da mutanen da zasu iya mutuwa a koda yaushe. Don haka wajibi mu zamo masu gaskiya,"

"Ya ku jam'ar jihar Legas, na kammala nazari kuma na yanke hukuncin zan canza yanayin shugabancin jihar nan. Dole ne mu bar duk abinda zai saka mana girman kai da tozarta damokaradiyya. Bazamu zamo iyayen gijin wadanda suka zabemu ba. A hakan da za muyi ne zai mika sako ga duk ma'aikatan jihar nan. Dole ne muyi biyayya ga zabin mutane, mu bauta musu kamar yadda suka zabemu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel