Zargin saba ka’ida: Majalisar wakilai za ta binciki yan majalisa na PDP 4

Zargin saba ka’ida: Majalisar wakilai za ta binciki yan majalisa na PDP 4

- An zargi wasu yan majalisa na PDP hudu da nuna kansu a matsayin manyan jiga-jigan jam’iyyar a majalisar wakilai

- An yi zargin ne lokacin da wani dan majalisa na PDP, Ben Igbakpa ne ya ja hankali game da lamarin a lokacin zaman majalisa

- Igbakpa ya ambaci sunayen Kingsley Chinda, Chukwuka Onyema, Umar Barde da Muraina Ajibola a matsayin wadanda ke daukar kansu a matsayin jiga-jigan jam’iyyar

Rahotanni sun kawo cewa ana shirin gudanar da bincike kan yan majalisa hudu daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar wakilai kan yawon nuna kansu a matsayin manyan jiga-jigan jam’iyyar.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa majalisar wakilan ta umurci kwamitinta kan da’a da ya binciki lamarin bayan Ben Igbakpa ya gabatar da lamarin a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba.

Igbakpa, dan majalisa na PDP daga jihar Delta, ya ambaci sunayen Kingsley Chinda, Chukwuka Onyema, Umar Barde da Muraina Ajibola a matsayin yan majalisar da ke yawan nuna kansu a matsayin manyan shugabannin jam’iyyar.

An rahoto cewa Chinda da mukkarabansa a kwanan nan sun saki akalla Jawabai uku a madadin manyan jiga-jigan PDP a majalisar.

KU KARANTA KUMA: Babban magana: Lauyoyin Edo sun kauracewa kotu kan sace wata mai shari’a

Bayan Ogbakpa ya gabatar da lamarin, mataimakin kakakin majalisa, Idris Wada, wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya umurci kwamitin da ya binciki lamarin sannan ya kawo wa majalisar rahoton.

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Fadar Shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin cewa akwai wani rashin jituwa a tsakanin ofishin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da na mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo.

Babban mai ba Shugaban kasa shawara na musamman akan harkokin majalisar dokokin tarayya, Sanata Babajide Omowurare ya bayyana hakan yayinda yake jawabi ga manema labarai a majalisar dokokin tarayya.

Da yake martani ga masu sukar lamari wadanda suka dasa ayar tambaya akan hukuncin shugaba Buhari na sanya hannu a wata doka a Landan, Sanata Omowrare ya ce lallai kundin tsarin mulki ta ba Shugaban kasar damar aiki daga ko ina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel