Kwallon kafa: Hassan zai dakata daga buga gasa saboda marin Alkali

Kwallon kafa: Hassan zai dakata daga buga gasa saboda marin Alkali

Kungiyar da ke kula da kwallon kafa a jihar Nasarawa, ta dakatar da ‘Dan wasa Yakubu Hassan wanda ya ke bugawa kungiyar kwallon kafa na Dubagari da ke Garin Lafiya a jihar Nasarawa.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto cewa Nasarawa FA ta hana Yakubu Hassan buga wasa a halin yanzu. An samu ‘dan kwallon kafan da laifin fyadawa Alkalin wasa mari ne a cikin fili.

Halidu Akwashiki, wanda shi ne mataimakin shugaban kungiyar, ya sanar da wannan ukuba da aka yi wa ‘dan wasan da ya aikata laifin. Akwashiki ya fadawa Manema labarai wannan dazu.

Da ya ke sanar da ‘yan jarida a hira, Mista Akwashiki, ya tabbatar da cewa Hassan na kungiyar Dubagari ya yanke Alkalin tsakiyar fili, Kasimu Ahmadu, ne da mari a 23 ga Watan Oktoba.

Wannan ya faru ne a lokacin da Dubagari ta Garin Lafia ta kara da kungiyar Winda Force da ke Nasarawa-Eggon. ‘Dan wasan ya mari Alkalin ne bayan an gargade sa sakamakon yin wani laifi.

KU KARANTA: Ministan wasanni ya koyawa Shugabannin NFF darasi

Mataimakin shugaban kungiyar kwallon ya ce wannan laifi ya yi masu ban-ba-ra-kwai don haka su ka kafa kwamiti domin a binciki ‘dan wasan. A karshe an haramta masa buga gasar da ake yi.

Bayan dakatar da ‘dan wasan daga gasan gaba daya, kungiyar ta FA ta kuma bukaci ‘dan kwallon ya rubuta takardar afuwa ga Alkalin da ya mara. Sannan kuma an ci kulob dinsa tarar wasu kudi.

Nasarawa FA ta shirya wannan gasa da ake bugawa tsakanin kungiyoyi 30. An raba kungiyoyin zuwa gidaje hudu. An take gasar ne a 30 ga Satumba wanda har aka zarce watan Oktoba ana yi.

“Matakin da mu ka dauka za su sauran ‘yan wasa su shiga taitayinsu, kuma kungiyoyi su daina tada rikici da Alkalan wasa, sannan su bi dokar kwallo.” Hukumar Alkalai ta koka da lamarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel