Majalisar dokokin jaha ta amince da nadin kwamishinoni 23 a gwamnatin Adamawa

Majalisar dokokin jaha ta amince da nadin kwamishinoni 23 a gwamnatin Adamawa

Majalisar dokokin jahar Adamawa ta tabbatar tare da amincewa da sunayen mutane 23 da gwamnan jahar Ahmadu Fintiri ya aika mata wadanda yake muradin nadasu mukamin kwamishinoni a majalisar zartarwar jahar.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito majalisar ta amince da sunayen da Gwamna Fintiri ya aika mata domin tantancewa ne bayan kwanaki 3 kacal da karbar jerin sunayen.

KU KARANTA: El-Rufai, Sarakuna, hafsoshin tsaro da yan majalisu sun goga gemu da gemu a kan tsaron Kaduna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban masu rinjaye na majalisar, Hammantukur Yettisuri ne ya fara gabatar da kudirin amincewa da sunayen sabbin kwamishinonin a gaban majalisar, inda daga bisani mataimakinsa, Japhet Kefas ya mara masa baya.

Daga nan kuma sai kaakakin majalisar, Aminu Iya-Abbas ya nemi jin ta bakin sauran yayan majalisar, inda dukkaninsu suka amince ba tare da wata matsala ba.

Daga cikin sabbin kwamishinonin akwai Adamu Atiku Abubakar, babban dan Atiku Abubakar, Abdullahi Parambe, Wilbina Jackson, Justina Nkom, Lami Patrick, Farfesa Isa Abdullahi da Mohammed Umar.

Sauran su ne Ibrahim Mijinyawa, Umaru Daware, Elijah Tumba, Ishaya Dabari, Sunday Mathew, Hassan Kaigama, Umar Garba, Usman Diyajo, Mustapha Jika, Sanusi Faruk, Bappa Isa, Aloysius Babadoke, Shuaibu Audu, Iliya James, Dishi Khobe da Adamu Titus.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi wasu sabbin nade naden hadimai masu muhimmanci a gwamnatinsa da zasu taya shi gudanar da ayyukansa da manufofinsa wajen cika ma jama’an jahar Kaduna alkawurran daya daukan musu.

Kaakakin gwamnan jahar Kaduna, Muyiwa Adekeye ne ya sanar da wadannan sabbin nade inda yace gwamnan Kaduna ya amince da nadin tsohon babban ma’aikacin jaridar Daily Trust, Malam Ibraheem Shehu a matsayin mataimaki na musamman a harkar kafafen watsa labaru da hulda da jama’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel