Takardu sun tabbatar Amosun ya sabawa doka wajen safarar makamai

Takardu sun tabbatar Amosun ya sabawa doka wajen safarar makamai

A Ranar 25 ga Watan Yuni, Sanata Ibikunle Amosun ya karyata zargin da Jaridar Premium Times ta yi masa na cewa ya shigo da makamai ta hanyoyin da ba su dace ba a lokacin yana gwamna.

Bayan karyata wannan zargi da Amosun ya yi, Jaridar ta sake komawa ta yi wani bincike na tsawon watanni inda ta tabbatar da cewa babu shakka tsohon gwamnan ya shigo da makamai.

Jaridar ta ce ta gano babu shakka, satifiket din da aka ba Ibikunle Amosun na shigo da wasu makamai 13 ne kacal. A karshen ya shigo da bindigogi 1, 000 da casbin harsashi miliyan hudu.

Abin da yanzu ba a gane ba shi ne ko tsohon gwamnan ya samu sa-hannun ofishin NSA kafin ya shigo da makaman. Amma dai tabbas hujjoji sun nuna gwamnatin Ogun ta sanar da ofishin.

KU KARANTA: Tambayoyin da ake bukatar Amosun ya amsa kan shigo da makamai

Amosun ya rubutawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan takarda a lokacin inda ya nemi a daga masa kafa daga biyan kudin shigo da kayan. Kuma haka ya shigo da duk makaman a bagas.

Tsohon gwamnan na Ogun ya samu damar shigo da makamai na fiye da biliyan 1. A ka’ida ya kamata ya ba asusun Najeriya Naira miliyan 209 a matsayin na ta kason na shigo da kayan waje.

Wani masanin harkar tsaro, Cheta Nwanze, ya sanar da Jaridar cewa ana iya shigowa da kaya cikin Najeriya ba tare da hukuma sun yi komai ba, wanda wannan ke tada wutar rikicin zabe.

Nwanze ya ke cewa irin wannan saba doka wajen shigo da kaya daga waje ya zarce bada cin hanci da rashawa, ya ce duk wani na-kusa da gwamnati ya na iya abin da ya ga dama a iyokokin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel