Zargin yi ma Buhari juyin mulki: Sowore ya cika dukkanin ka’idojin samun beli

Zargin yi ma Buhari juyin mulki: Sowore ya cika dukkanin ka’idojin samun beli

Masu iya magana na cewa “Da kyar na sha ya fi da kyar aka kama ni” daga karshe mawallafin kamfanin jaridar yanar gizo ta Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya cika dukkanin sharuddan beli da wata babbar kotun tarayya ta gindaya masa.

Jaridar Punch ta ruwaito babban lauya, Femi Falana ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba, inda yace Omoyele Sowore tare da abokina Olawale Bakare sun cika sharuddan beli a kan tuhume tuhumen cin amanar kasa da gwamnatin Najeriya take musu.

KU KARANTA: El-Rufai ya kara nada sabbin hadimai guda 18 a fadar gwamnatin Kaduna

Falana yace da wannan yake fatan kotun za ta bada umarni ga gwamnati da ta sakesu dukkansu a yau Laraba, 6 ga watan Nuwamba domin komawa ga iyalansu bayan kwashe fiye da kwanaki 90 a hannun hukumar DSS.

“Na fada ma lauya ma shigar da kara cewa muna fuskantar tasgaro wajen shirya kariya ga wadanda muke karewa sakamakon hukumar DSS ta ki bamu daman tattaunawa dasu, amma tunda sun cika sharuddan beli, muna sa ran da zarar DSS ta sake su zamu fara shirya kariya a garesu.” Inji shi.

Idan za’a tuna, a kwanakin baya ne wata babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Abuja ta sassauta sharuddan belin da ta gindaya ma shugaban kawo juyin juya hali a Najeriya, kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters.

Alkalin kotun, Ijeoma Ojukwu ce ta yanke wannan hukunci a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba inda tace ta rage masa kudin beli naira miliyan 100 da ta sanya masa zuwa naira miliyan 50, sa’annan ta rage sharadin beli na naira miliyan 50 ga Bakare zuwa naira miliyan 20.

Haka zalika Alkali Ojukwu ta sassauta sharadin cewa lallai sai masu tsaya ma mutanen biyu sun ajiye shaidan suna da kwatankwacin wannan kudi a asusunsu da kotu, inda tace ta janye wannan sharadin shima.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel